SUBUL-DA-BAKA: A yafe min cewa da nayi yara 10 kacal aka sace – Garba Shehu

0

Babban Mai Taimakawa Ga Shugaba Muhammadu Buhari a Fannin Yada Labarai, Garba Shehu, ya nemi afuwar subul-da-bakan da ya yi cewa yara 10 aka sace a Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Kankara, a jihar Katsina.

PREMIUM TIMES ta buga Labarin yadda aka sace yara sama da 300 cikin dare, a ranar 11 Ga Disamba, ranar da Shugaba Buhari ya isa jihar domin fara hutun mako daya.

Yayin da Gwamna Masari ya bayyana cewa yara 333 ne aka sace, Shehu ya bayyana cewa yarann su 10 ne.

Bayan kwanaki shida an sako yaran, wadanda kididdiga ta nuna su 344 ne, fiye ma da adadin 333 da Masari ya bayyana da farko, kuma fiye da adadin 10 da Shehu ya bayyana.

Wannan ya sa kakakin na Shugaban Kasa Garba Shehu fitowa ya nemi afuwa, tare da yin karin bayanin cewa wasu da ya kamata a ce sun san takakaimen adadin ne su ka bayyana masa cewa 10 ne aka sace.

Ina Neman Afuwa – Garba Shehu

“Ina mai neman afuwa dangane da kuskuren da na yi, inda na ce adadin daliban Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Kankara (GSSS) da aka yi garkuwa da su, su 10 ne.

‘‘Ba da gangan na yi wannan furucin ba. Na samu wannan bayani da na sanar a lokacin, daga bakin wadanda ya kamata a ce sun san hakikanin adadin kafin su sanar da ni cewa su 10 ne.

“Dalili kenan aka ga adadin yawan da na furta, ko kusa bai kai yawan wadanda ake cigiya ba a lokacin.

“Tare da neman afuwa, ina so a fahimci ban isar da wancan sako ba domin rage yawan su da gangan.

‘‘Ina rokon a karbi uziri na kan wannan lamari. Mu ci gaba da kokarin da mu ke a kai na ganin mun maida Najeriya Kasaitacciyar Kasa.”

Bayanin Shehu kenan wanda ya watsa a shafin san a Facebook sa sauran shafukan sada zumunta.

Tuni dai yaran aka damka su a hannun iyayen su, bayan sun gana da Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Masari.

Ita ma Shugabar Hukumar Kula da ‘Yan Najeriya Mazauna Kasashen Waje, Abike Dabire, ta yi subul-da-bakan cewa an sako yaran, tun kafin a sake su.

Ta yi furucin ne a shafin ta na Twitter, inda daga baya ta yi ikirarin cewa, masu kutse ne su ka shiga shafin su ka yi rubutun, ba da sanin ta ba.

Share.

game da Author