Sojojin Najeriya sun kashe Boko Haram 20 tare da kama ganimar manyan makaman su, lokacin da su ka yi yunkurin kai mummunan hari garin Askira Uba, a Jihar Barno.
Ado Isa, Mataimakin Daraktan Yada Labarai na Runduna ta 7 da ke Barno ne ya fitar da wannan sanarwa, a ranar Lahadi.
Ya ce zaratan sojojin Najeriya sun afka wa maharan Boko Haram da kisa tare da lalata masu motoci da makamai.
” Musamman wata babbar nasara da dakarun mu su ka yi kan Boko Haram, ita kama motoci hudu masu daukar bindigogin igwa da kuma lalata wasu motocin irin su.
“An kashe Boko Haram da dama, amma dai da idon mu mun kirga gawarwaki 20, banda wadanda aka ji wa ciwo.
“An kama bindigogin harbo kananan jirage uku, wasu manyan bindigogi hudu sai manyan bindigogi kirar Tashi-gari-barde (RPG) guda 13.”
Sai dai kuma ya ce an kashe soja daya, wasu biyu kuma sun samu rauni. Amma dai ya ce ana kulawa da su a asibiti, su na kuma samun sauki.
Yayin da ya ke addu’ar samun rahama daga Allah ga sojan da ya rasa ran sa, Isa ya ce sojojin Najeriya a karkashin Laftanar Janar Tukur Buratai ba za su gajiya ba har sai sun kakkabe burbushin ‘yan ta’addar da ke yankin Arewa maso Gabas.