Sojoji sun kama mahara 12 a jihar Zamfara

0

Sojin Najeriya dake aiki a karkashin rundunar ‘Operation Hadarin Daji’ sun Kama mahara 12 a jihar Zamfara.

Kodinaton yada labaran rundunar Sojin Najeriya John Enenche ya sanar da haka a wata takarda da aka raba wa manema labarai ranar Talata.

Ya ce sojojin sun Kama wadannan mahara a kauyukan Magizawa, Kani, Zango, Tabanni da Nasamu dake karamar hukumomin Kauran Namoda ranar Litini.

Enenche ya ce dakarun sun Kama wadannan mahara ne bayan sun samu labarin ta’addancin da suke tafkawa a wadannan kauyuka.

Ya ce sun kashe mahara da dama sannan wasu sun gudu da raunin harsashi a jikinsu.

Kuma sun kwato harsasan bindiga da bindigogi da dama a wannan arangama.

Bayan haka Enenche ya ce dakarun sun kama mota kirar J5 dankare da baburan hawa har guda 20.

Bincike ya nuna cewa direban motar da kwandastan sa sun yi dakon wadannan babura za su kai su inda maharan ke sheke ayarsu a dajin Jibia.

Daga nan kuma sojojin sun kama barayin shannu a kauyen Raudama.

Idan ba a manta ba har yanzu dai ana zaman juyayi sace daliban makarantan kwana dake Kankara, Jihar Katsina.

A ganawa da PREMIUM TIMES HAUSA suka yi da iyayen yaran dake zaune gaban makarantan sun koka kan yadda rashin tsaro yaki ci yaki cinyewa a musamman yankin jihar Katsina.

Sun yi kira ga gwamnati ta gaggauta ceto yaran daga hannun maharan.

Share.

game da Author