Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu Alaikum
Jiya Talata, Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya sheka wata irin karya, wadda ina mai yi maku rantsuwa da Allah cewa shi da yake fadar maganar yasan cewa karya yake yi, haka wallahi, duk wadanda suke sauraronsa a lokacin da yake fadar maganar, sun san da cewa karya yake yi, shi yasa ma a lokacin da yake bayanin, suna ta yi masa dariya, sun mayar da shi gabo, amma da yake shi wani irin mutum ne marar fahimta, sai bai gane manufar dariyar tasu ba. Ya dauka cewa dariya ce ta nuna goyon baya, alhali ba haka bane, wallahi dariya ce ta sun nuna suna sauraron mutumin da yake karanta masu wata irin tatsuniyar gizo-da-koki mai dadin sauraro!
Abun mamaki, wai su har yanzu wadannan mutane ba su daina maganar Sarki Muhammadu Sanusi II ba. Wai shi saboda su Goodluck Jonathan su so shi.
Alhali shi kuma Sarki yayi gaba, bai ma san da su ba, amma su suna ta hauka. Har yanzu ya tsone masu ido, sun ga yana ta ci gaba, kuma farin jinin sa kullun gaba yake yi, shine suke cikin rudewa da damuwa game da shi a koda yaushe!
Tun lokacin da suka sauke Sarki Muhammadu Sanusi II, babu wanda ya taba ji yayi wata magana a kan su, saboda basu ne a gaban sa ba. Harkokin sa yake yi da sha’anin gaban sa, amma su suna nan ya tsone masu ido. Yau su ce wannan, gobe su ce wannan!
Kamar yadda wasun ku suka ji, ko suka gani, ko kuma suka sani, a wurin kaddamar da wani littafi da wani dan jarida mai suna Bonaventure Philips Melah ya rubuta akan tsohon shugaban kasar Najeriya, wato Goodluck Ebele Jonathan (GEJ), Gwamnan Kano ya baro wani shirme, wanda ko jahilin jahilai yasan ba gaskiya ba ne, kawai karya ce da son zuciya tsagwaronsa. Kuma duk wadannan maganganu kamar yadda kowa ya sani, ya fade su ne saboda neman goyon bayan ‘yan kudu, kamar yadda ya saba yi. Misali, ya mayar da su Tinubu da ‘yan kudu Allolinsa, yana ganin cewa wai zasu iya kare shi idan ya sauka daga kan mulki!
Yo in ban da shirme ma, don Allah me ya kawo maganar cire Sarki a wurin kaddamar da littafi kan Goodluck Ebele Jonathan? Kawai wannan shaida ce da ke nuna cewa wannan mutum a rude yake kenan!
Wai Ganduje, babu kunya babu tsoron Allah yake cewa, ya cire Sarki Muhammadu Sanusi II ne domin ya ceto masarautar Kano daga lalacewa!
Yanzu don girman Allah, duk kokarin da Sarki Muhammadu Sanusi II yayi a cikin shekaru shida da Allah ya kaddari yayi bisa gadon sarauta, na farfado da martabar masarautar Kano, ya gyara gidan Dabo, ya taimakawa fadawa da ma’aikatan fada, ya taimaki talakawan masarautar Kano, ya hada kan zuri’ar Dabo, ya sadar da zumunci, baki sun shigo Kano sun kawo cigaba, wanda duk duniya ta shaida haka, Ganduje yana nufin ya wofintar da hankulan mutane, su kasa fahimtar inda ya nufa kenan? Haba Malam, ai ko wawa ba zai taba yadda da maganganun Ganduje ba wallahi, bare mutum mai cikakken hankali!
Kuma wai babu kunya babu tsoron Allah, Ganduje yake cewa wai Sarki Muhammadu Sanusi II bai cancanci zama Sarki ba, a lokacin da aka zabe shi, a shekarar 2014, wai kawai an dora shi ne domin a rama masa abunda shugaba Jonathan yayi masa, ko kuma wai domin aci mutuncin Jonathan! Yanzu don Allah irin wadannan mutane sune manya, alhali manya an sansu da nuna halin girma na samar da zaman lafiya, da hada mutane, da yin sulhu, ba zuga mutane, da haddasa adawa da kiyayya tsakanin mutane ba?
Jama’ah wannan ma wallahi kun san cewa karya ce tsagwaronta, wai wani mutum ya fito yana shaida wa duniya cewa Sarki Muhammadu Sanusi II bai cancanci hawa gadon sarautar Kano ba, kawai saboda muguwar hassada da bakin ciki da ke zuciyar sa! To har idan bai cancanta ba, don Allah waye zai cancanta? Sai a fada muna!
Duk duniya ta shaida cewa, hawan Sarki Muhammadu Sanusi II kan sarautar Kano, masarautar Kano ta bunkasa sosai. Baki daga ko’ina cikin duniya, sai kwarara suke yi zuwa jihar Kano, domin an dora mutum wayayye, mai ilimi, mai hakuri, mai tawali’u, mai son jama’ah, wanda ba dan-amshin-shata ba akan gadon sarauta! Amma don Allah muyi wa kawunanmu adalci, shin tun da aka cire shi, masarautar Kano taci gaba ko taci baya ne? Duk duniya dai tana kallon abunda yake faruwa, don haka sai mu amsa wa kan mu wannan muhimmiyar tambaya!
Sannan kudin da Sarki Muhammadu Sanusi II yace an sata, ko sun bata, lokacin da yake Gwamnan babban bankin Najeriya, a lokacin mulkin shugaba Jonathan, shin karya ne ba’a yi ba? Karya ne basu bata ba? Idan ba gaskiya bane, to duniya tana sauraron Gwamna Ganduje ya fito yayi muna cikakken bayani! Ai duk wani dan halal, wallahi kamata yayi ya jinjina wa Sarki Muhammadu Sanusi II, a bisa namijin kokarin da yayi, da jajircewarsa wurin ceto kasarnan, a wancan lokacin. Bawan Allah nan ya sadaukar da rayuwarsa, ya sadaukar da kujerarsa ta babban Gwamnan banki, yayi fatali da duk wani gata da jin dadi na kujerar shugabanci, ya fadawa duniya gaskiyar abunda yake faruwa. A lokacin, da yaso, da sai yayi shiru, aci kudin da shi, amma ya nuna shi baya son kudi masu datti da kazanta irin wadannan. Ya gwammace gara ace ya sauka daga mukaminsa, ya hakura da shi, domin ya ceto kasar sa! ‘Yan uwana masu daraja, wallahi, wallahi, wallahi ba kowa ne zai iya yin jarunta irin haka ba a yau!
Kuma wai Ganduje yace a lokacin kamata yayi, Sarki Muhammadu Sanusi II, da ya gano wannan barna, sai ya fadawa Jonathan a sirrance, su shawo kan matsalar, ba tare da kowa yaji ba.
Amma shi Ganduje ya manta da cewa, Sanusi ya shaidawa duniya cewa, ya fadawa Jonathan, kuma yayi-yayi a saurare shi, ko a dauki matakin da ya dace, amma aka ki, shi yasa shi kuma ya fallasa barnar, domin ya sauke nauyi da alkawarin da ya daukar wa ‘yan Najeriya, cewa zai yi aiki bisa gaskiya da adalci, kuma tsakani da Allah!
Sannan wallahi duk duniya ta shaida cewa Kanawa suna son Sarkin su, suna kaunar sa, domin a lokacin da ‘yan-bani-na-iya suka hadu, suka yi masa ta’addaci, suka cire shi, duniya ta shaida yadda Kanawa suke kuka, suka shiga halin tsahin hankali da damuwa da dimuwa, amma suka yi hakuri, a bisa jan kunne, da gargadi, da kiran da Sarki Muhammadu Sanusi II yayi masu na cewa don girman Allah, duk wani masoyinsa ya zauna lafiya, a dauki kaddara, kar wanda ya tayar da hayaniya, ko fitina, ko yayi wani rikici ko tashin hankali saboda an sauke shi daga sarauta.
Kowa ya shaida Sarki mutum ne mai son zaman lafiya. Kuma da yake masoyansa suma mutane ne masu biyayya, sai suka saurare shi, suka bi umurninsa, basu tayar da ko wace irin rigima ba. Amma sai wawaye da jahilai suka dauka cewa wannan rashin tayar da hankalin kamar wai Sarki Muhammadu Sanusi II baya da kowa ne. Dibgaggu kawai! Wallahi da ace masoyan Sarki fitinannu ne da suna iya tayar da jihar Kano baki daya, amma da yake su mutane ne masu kishin Kano, masu kishin arewa da Najeriya baki daya, kuma duk wata hayaniya zaka tarar da cewa su basa cikinta!
Saboda haka, muna kira ga Gwamna Ganduje da ya shiga taitayinsa, kuma ya ja bakinsa yayi shiru. Domin shi da Sarki Muhammadu Sanusi II, yasan cewa ruwa ba sa’ar kwando ba ne.
Ai yanzu dai gashi nan, wadannan maganganu na kwaba da yaje yayi a wurin kaddamar da wannan littafi na Jonathan, sun jawo masa la’ana da tsinuwa da Allah waddai a wurin ‘yan Najeriya! Idan mutum mai bibiyar kafafen yada labarai na zamani ne, wato soshiyal midiya, to zai ga abun da nike nufi!
Jami’ar Ingila ta gayyaci Sarki Muhammadu Sanusi II domin ya kaddamar da wani karatu, kuma ya taimaka masu akan wasu abubuwa, amma saboda hassada da bakin kishi, shima Ganduje ya tafi wurin yayi karma-karma don ya tafi wata Jami’a a Amerika, wai shima ya zama farfesa, shine ya hadu da ‘yan 419, ‘yan damfara, suka yi masa wayo, suka damfare shi! Bawan Allah kayi hakuri, shi matsayi da girma da daukaka duk daga Allah ne, idan Allah ya daga mutum wallahi babu mai iya dankwafar da shi, haka idan kuwa Allah bai daga ka ba, babu mai iya daga ka sama!
Daga karshe ina mai cewa Alhamdulillahi, muna godiya ga Allah, da ya sanya duniya ta shaida cewa Sarki Muhammadu Sanusi II mutum ne mai gaskiya, mai kaunar Najeriya da arewa, mai son talakawa, kuma mai kishin su. Sannan bayan wannan, duniya ta shaida cewa shi ba barawo bane! Alhamdulillahi game da wannan.
Kuma Ganduje da mutanen sa sun sani, duk wata karya da batanci da sharri da kage da zasu yi akan Sarki Muhammadu Sanusi II, sun san da cewa duniya ba zata yarda da su ba. Yanzu ma maganar da ake yi shine, suyi kokari su wanke kansu, maimakon kokarin yiwa wasu sharri da karya. Wannan shine!
Kuma me yasa ne sai yanzu Ganduje yake cewa Sarki Muhammadu Sanusi II bai cancanta ba, ko bai fadi gaskiya ba? Ko don yayi-yayi ya juya Sarki Sanusi ya bi son zuciyarsa yaki yarda, shine zai canza magana yanzu? Ganduje fa ya sani, muna da bayanin da yayi a baya game da Sarki Muhammadu Sanusi II. Zan sa bayanin sa a nan yadda yazo a kafar yada labarai, da turanci, ba tare da na canza, ko na fassara shi ba. Gwamna Ganduje yake cewa:
“Sanusi was the best among the candidates to be appointed as Emir of Kano. His wealth of experience as one of the best economics today in the world, and his trust is always his weapon, remember how he exposed how billion of dollars was stolen by some person under President Jonathan administration. I congratulate His Excellency Governor Rabi’u Kwankwaso for choosing a right person at a time Kano and Nigeria need people like Sanusi Lamido Sanusi at this position.” Kano state Deputy Governor, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, on Friday 13th June, 2014, at Kano Government House, Friday Mosque, during Friday prayer, live on Channels TV and Freedom Radio.
Jama’ah yanzu sai ku zama alkalai, sai ku yanke hukunci na gaskiya, mai cike da adalci. Ga maganar da Ganduje yayi a can baya game da Sarki Muhammadu Sanusi II, sannan ga maganganun da yake yi ayau. Daga karshe zaku fahimci waye Ganduje!
A yau muna cikin mulkin Dimukradiyyah ne, idan kayi karya domin ka ci mutuncin wani, to Allah zai kawo wadanda zasu fayyace gaskiya, domin kowa ya gane cewa kai makaryaci ne. Saboda doka ta bai wa kowa damar yayi magana, kuma ta bai wa kowa ‘yanci fadin albarkacin bakin sa a kasar nan!
Wassalamu Alaikum
Dan uwanku: Imam Murtadha Muhammad Gusau ne ya rubuta daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun Imam a lambar waya kamar haka: 08038289761.
Discussion about this post