An bayyana sanarwar rasuwar Sanata Saidu Kumo, wanda ya rasu ranar Lahadi da safe, kamar yadda dan sa Abubakar ya shaida wa PREMIUM TIMES.
Kumo ya rasu ya na da shekara 71 a duniya.
Ya rasu a asibitin Gwagwalada, inda ya ke jinyar rashin lafiya.
Kumo yayi sanata tsakanin 1999 zuwa 2003, inda ya wakilci Mazabar Gombe ta Tsakiya, karkashin jam’iyyar APP, wadda daga baya ta koma ANPP.
Ya rike mukamin mashawarci na musamman ga tsohon Shugaban Kasa, Umaru Yar’Adua na wani takaitaccen lokaci, a cikin 2008.
Saidu Kumo yaya ne ga Tsohon Ministan Babban Birnin Tarayya, Aliyu Modibbo, Danburam Gombe.
Allah ya gafarta wa Saidu Kumo, amin.
Discussion about this post