Sabani wajen rabon ganima tsakanin ‘yan bindiga yayi sanadiyyar ran kasurgumin dan ta’adda a dajin Kaduna

0

Rabon ganimar da aka kwace a hannun mutane ya tada zaune tsaye a tsakanin wasu kungiyoyin ‘yan bindiga da suka addabi dazukan dake kewayen Kaduna wanda a sanadiyyar rashin jituwar ya sa sun karkashe juna, ciki har da nasiru Kachalla.

A dalilin kaurewa da rigima da suka yi an kashe kasurgumin dan ta’adda da ya addabi jihar Kaduna da kewaye, Nasiru Kachalla.

A sanarwan da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Kaduna Samuel Aruwan ya fitar ranar Litinin, ya bayyana cewa rigima ya kaure a tsakanin bangarorin biyu a cikin daji a lokacin da suke kokarin raba wasu shanu da dabbobi suka kwace da karfin tsiya wajen wasu makiyaya.

A wajen rabon ne fa rigima ya kaure, gaba dayan su suka bude wa juna wuta. ‘yan wannan bangaren da wancan bangaren.

Sanarwar ta ce an kashe wa kowa mayaka.

” Rikicin ya kaure ne a dajin dake tsakanin Kajuru da Chikun. Kachalla da abokan aikata ta’addancin su sun dade suna addabar mutanen kauyukan Kaduna. An gano cewa sune suka taba sace yaran makaranta a karamar hukumar cikun.

” Sai dai kuma an kama wasu daga cikin manyan abokan aikin sa uku, shine dai ba a kama ba wato Nasiru Kachalla.

Aruwan ya kara da cewa jami’an tsaro sun fatattaki wasu mahara da ke tare hanyar Zariya zuwa Giwa suna sace mutane. ” Maharan sun tare hanya suna harbi ta ko ina, wasu da dama sun bace, amma kwamishina Aruwan ya ce ana nan ana farautar maharan da wadanda suka bace a dajin.

Share.

game da Author