Femi Adesina, Kakakin Yada Labarai na Shugaba Muhammadu Buhari, ya ce ‘yan Najeriya su gode wa Buhari, duk da halin da ake ciki, domin shugaban ya yi matukar kokari wajen samar da zaman lafiya a fadin kasar nan.
Da ya ke bayani a cikin wani shiri da ya bayyana a Channels Talbijin, Adesina ya ce Najeriya ta samu kan ta cikin halin rashin tsaro, kamar yadda sauran kasashe da dama na duniya su ka tsinci kan su a ciki.
Adesina ya ce duk da abubuwan da su ka faru na sace dalibai 424 cikin mako daya tak, da kuma kashe-kashen da ke faruwa a wasu sassan kasar nan, Buhari na samun galaba a fannin yaki da rashin tsaro.
“Ana samun nasara sosai a kan tsaro. Domin akwai lokacin da za a shafe kwanaki ko makonni, ko wata ba tare da samun rahoton rashin tsaro ba.
A baya fa kada mu manta, a kullum sai an samu rahoton tashin bama-bamai a kasar nan. Wannan tashin bom da ya faru kwanan nan, idan ka duba sai ka ga an dade ba a ji labarin tashin bomb a. A shekarun gwamnatin baya kuwa a kullum sai ka ji tashin bom kamar ana buga –nok-awut.”
“A da can a kullum bom na tashi sau biyar ko sau shida. Amma yanzu sai a yi wata biyu ko uku bom bai tashi ba. saboda haka mu gode wa Allah dangane da wannan sauki da ya samar mana. Kada mu zama marasa godiya ga Allah, ba mu fadin alheri sai sharri kawai.
Adesina ya roki ‘yan Najeriya su kara hakuri, kada su ba Buhari lokaci ko wa’adin da zai kawar da matsalar tsaro a kasar nan.
“Ba Najeriya kadai ce kasar da ke fama da matsalar tsaro ba. Abin ya ma zama ruwan-dare, ya game duniya. Hatta manyan kasashe na duniya na fama da wannan matsala.”
Sace yara 344 da aka yi a Kankara Jihar Katsina, da kuma sace wasu 80 a Katsina din, a ranar da aka damka wadanda aka kubutar daga masu garkuwa, ya kara dagula harkar tsaro a kasar nan, wadda ta kara gigita duniya, a lokacin da Boko Haram su ka yi wa manoma 43 yankan-rago a Zabarmari, Jihar Barno.
Discussion about this post