RASHIN TSARO: Jihohin Kaduna da Zamfa ne aka fi kashe ‘yan sanda cikin shekaru shida -Rahoto

0

Wani rahoton bin-diddigi ya bayyana cewa tsawon shekaru shida kenan an fi kashe jami’an ‘yan sanda a jihohin Kaduna da Zamfara, wato daga farkon 2015 zuwa karshen 2020.

Rahoton dai mai suna Yadda Ake Kai Wa ‘Yan Sanda Farmaki, cibiyar binciken kwakwaf ta SBM Intel ce da ke Lagos, ta fitar da shi.

Rahoton wanda SBM Intel ya fitar, ya nuna babu jihar da ba a kashe dan sanda ba a fadin kasar nan, tsakanin 2015 zuwa yanzu karshen 2020.

Rahoton ya kuma nuna cewa wasu jami’an ‘yan sandan a ofishin su aka yi masu takakkiya aka kashe su. Yayin da wasu kuma a lokacin da su ke kan aikin su na tabbatar da bin doka da oda.

Sai dai kuma rahoton ya ci gaba da bayyanawa dalla-dalla cewa a yayin da hakan ke faruwa, tsautsayi na ritsawa ta kan mai tsautsayi har a dirka masa bindiga.

“Wadanda harsashe kan kashe a bisa tsautsayi idan an yi harbi, sun ma fi yawan ‘yan sandan da aka kashe.

Jihar Kaduna: Rahoton ya ce cikin shekaru shida an kashe ‘yan sanda 360 a jihar Kaduna.

Jihar Zamfara: A Jihar Zamfara kuwa an kashe dan sanda 290 tsawon shekaru shida.

Yawancin asarar rayukan ‘yan sandan na zuwa ne sakamakon arangama da ‘yan bindiga.

Jihohin Kebbi, Bauchi da Jigawa ne ba a samu asarar rayukan ‘yan sanda masu yawa ba. Domin kowacen su an samu asarar ran dan sanda tsawon shekaru shida.

Jihar Delta an kashe 44, Ribas 38, sai kuma Edo 30.

Rahoton ya ce a duk mutum 600 na al’ummar Najeriya, akwai dan sanda 1 tal mai kula da su.

Share.

game da Author