Rahotanni sun tabbatar da cewa an yi garkuwa da wasu Indiyawa su biyu a Jihar Oyo da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.
An yi garkuwa da su ne a ranar Laraba, yayin da su ka fito daga kamfanin da su ke aiki a mota, za su hau babban titin Ibadan zuwa Lagos.
Har ya zuwa lokacin da ake rubuta wannan labari dai ba a san inda Indiyawan su biyu su ke ba.
An yi garkuwa da su karfe 4 na yamma, bayan an bi su da mota an bude masu wuta.
Matsalar garkuwa da mutane dai ta zama ruwan dare kuma mummunar sana’a a Najeriya, saboda makudan kudaden fansa da ake karba.
Ko a ranar Juma’a tsakar dare ‘yan bindiga sun sace daliban sakandare a makarantar kwana da ke Kankara, a jihar Katsina.
Yayin da ba a san adadin wadanda aka sace ba, ana zaton an tattara dalibai kimanin 340 zuwa 450 duk an shiga daji da su.
An sace su ne sa’o’i biyar bayan isar Shugaba Muhammadu Buhari Daura, a jihar Katsina, domin yin hutu na sati daya.
Har zuwa lokacin rubuta wannan labari dai babu labarin gano daliban.
Discussion about this post