RASHIN TSARO: An yi garkuwa da mutum 22 a jihar Neja

0

Wasu mahara dauke da muggan makamai akan babura sun yi garkuwa da mutum 22 a kauyukan Ogu da Tegina a jihar Neja.

Bisa ga rahoton da gidan talabijin din ‘Channels’ ya wallafa wani mazaunin kauyen Ogu, Kamal Wayam ya ce maharan sun far wa kauyen ranar Lahadi suna harbi da bindiga ta ko-ina.

“Sun shiga cikin gidajen mutane sun saci kaya sannan suka sace mutum shida, ciki hudu ‘yan gida daya ne, biyu kuma baki ne.

A safiyan Litinin kuma sai maharan suka far wa kauyen Tegina da misalin karfe 12.

A wannan kauye maharan sun yi garkuwa da akalla mutum 16.

Wani mazaunin kauyen mai suna Sani Gamachindo ya ce maharan sun shiga gidan ‘yarsa inda suka cinye dan sauran abincin da suka ci suka rage.

“Maharan basu yi garkuwa da kowa ba a gida saboda ‘ya ta ta boye a karkashin gado sannan mijin ta ya boye a cikin silin.

Yin garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a yankin Arewacin Najeriya. A ranar Asabar ne gwamnan Jihar Katsina Aminu Masari ya bada umarnin rufe dukkan makarantun kwanan Jihar Katsina, bayan ‘yan bindiga sun arce da daliban da ba a san adadin su ba.

Masari ya bada umarnin ne bayan da mahara da aka hakikance sun kai su 300 a kan babura suka kutsa sakandaren kwana ta garin Kankara, a Jihar Katsina.

Sun kutsa cikin makarantar wajen 11:30 na dare bayan sun harbe jami’in tsaro a kofar makarantar.

Masari ya kara tabbatar da cewa gwamnati za ta yi dukkan kokarin kawo karshen masu garkuwa da jama’a a jihar Katsina.

Share.

game da Author