RASHIN TSARO: An rufe makarantun Zamfara, Jigawa da Kano ba shiri

0

Jihar Kano ta bi takwarorin ta na Jigawa da Zamfara, inda ta bayyana kulle makarantun jihar, biyo bayan arcewa da dalibai 333 daga sakandaren Kankara, ta Jihar Katsina.

A ranar Talata ce Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano ya umarci a kulle dukkan makarantun jihar ta Kano da gaggawa.

Dama kuma an bada rahoton rufe makarantu a jihohin Jigawa da Zamfara, bayan sace dalibai 333 a Kankara.

Kwana daya bayan sace daliban Kankara, shi ma Gwamna Aminu Masari nan take ya bada umarnin kulle dukkan makarantun jihar ta Katsina.

Kwamishinan Harkokin Ilmi na Kano, Sanusi Kiru ne ya bayyana labarin rufe makarantun ga PREMIUM TIMES.

Kwamishinan ya umarci iyayen yara su garzaya makarantun su dauko ‘ya’yan su a safiyar Laraba.

Duk da dai bai bayyana dalilai ba, amma ana ganin cewa an rufe makarantun ne sakamakon sace dalibai 333 da aka yi a Katsina.

Dama dai a ranar 18 Ga Disamba ce, wato Alhamis za a rufe dukkan makarantu bayan kammala jarabawa.

BOKO HARAM Sun Ce Yaran Na Hannun Su

Cikin wani bidiyo da aka nuno Shekau na magana, wanda jaridar HumAngle mai bada labarin matsalar tsaro ta yi ikirarin samu, Abubakar Shekau ya ce su su ka kama daliban Kankara.

“Mun kama yaran Katsina domin mu daukaka addinin Musulunci kuma mu kashe wa zukata ci gaba da karatun boko. Saboda karatun boko dai Allah bai yi umarni a yi shi ba. Shi ma Annabi bai yi uarni a yi karatun boko ba.” Haka HumAngle ta ruwaito Shekau na ikirari.

Share.

game da Author