RASHIN TSARO: An kashe mutum 349, an yi garkuwa da mutum 290 cikin Nuwamba – Rahoto

0

Wata kungiyar bin kwakwafin kashe-kashe da garkuwa da mutane mai suna Nigeria Mourns, ta wallafa rahoton cewa cikin watan Nuwamba an kashe mutum 349, aka yi garkuwa da mutum 290 a yankuna daban-daban na Najeriya.

Rahoton wanda ya fito da filla-fillar adadin da rahotanni su ka nuna an kashe ko an yi garkuwa da su a cikin 2020, Nigeria Mourns ta ce amma ta kididdige adadin wadanda jaridu su ka buga kadai.

Kenan adadin wadanda aka kashe din da wadanda aka sace, ba ya dauke da wadanda jaridu ba su buga ba.

A yankunan karkara dai a kullum ana kisa kuma ana yin garkuwa da mutane, ba tare da kafafen yada labarai sun sani ba.

Sannan kuma rahoton ya nuna an tattaro bayanan alkaluman wadanda aka kashe din da wadanda aka yi garkuwa da su, a jihohi 23 daga cikin jihohi 36 da FCT Abuja.

Alkaluman sun nuna mutum 309 da aka kashe cikin watan Nuwamba duk fararen hula ne, yayin da 40 kuma duk jami’an tsaro ne.

Ga Adadin Su Dalla-dalla

Borno – 162, Edo – 57, Kaduna – 55, Katsina -12, Delta – 11, Zamfara – 10, Oyo – 5, Ondo – 5, Enugu – 4, Kogi -3, Kano – 3, Ekiti – 3, Adamawa – 3, Bayelsa – 3, Cross River – 2, Nasarawa – 2, Niger – 2, Rivers – 2, FCT – 1, Akwa Ibom – 1, Ebonyi – 1, Ogun – 1 and Sokoto – 1.

Rahoton ya ci gaba da cewa Boko Haram sun kashe mutm 149 cikin watan Nuwamba, yayin da ‘yan bindiga su ka bindige mutum 86, saura mutum 62 da aka kashe kuma duk wurin fadace-fadacen ‘yan kungiyar asiri ne.

Wasu 40 a fadace-fadace daban-daban aka kashe su, sai mutum bakwai kuma jami’an tsaro ne su ka bindige su ba tare da an zartas da hukuncin kisa a kan su ba.

Sai dai kuma duk da wannan kashe-kashe da satar mutane barkatai, Kakakin Yada Labarai na Shugaba Buhari, Femi Adesina, ya ce ’yan Najeriya su gode wa Buhari, duk rintsi dai yanzu an daina jefa bama-bamai

Femi Adesina, Kakakin Yada Labarai na Shugaba Muhammadu Buhari, ya ce ’yan Najeriya su gode wa Buhari, duk da halin da ake ciki, domin shugaban ya yi matukar kokari wajen samar da zaman lafiya a fadin kasar nan.

Da ya ke bayani a cikin wani shiri da ya bayyana a Channels Telebijin, Adesina ya ce Najeriya ta samu kan ta cikin halin rashin tsaro, kamar yadda sauran kasashe da dama na duniya su ka tsinci kan su a ciki.

Adesina ya ce duk da abubuwan da su ka faru na sace dalibai 424 cikin mako daya tak, da kuma kashe-kashen da ke faruwa a wasu sassan kasar nan, Buhari na samun galaba a fannin yaki da rashin tsaro.

“Ana samun nasara sosai a kan tsaro. Domin akwai lokacin da za a shafe kwanaki ko makonni, ko wata ba tare da samun rahoton rashin tsaro ba.

A baya fa kada mu manta, a kullum sai an samu rahoton tashin bama-bamai a kasar nan. Wannan tashin bom da ya faru kwanan nan, idan ka duba sai ka ga an dade ba a ji labarin tashin bomb a. A shekarun gwamnatin baya kuwa a kullum sai ka ji tashin bom kamar ana buga –nok-awut.”

“A da can a kullum bom na tashi sau biyar ko sau shida. Amma yanzu sai a yi wata biyu ko uku bom bai tashi ba. saboda haka mu gode wa Allah dangane da wannan sauki da ya samar mana. Kada mu zama marasa godiya ga Allah, ba mu fadin alheri sai sharri kawai.

Adesina ya roki ‘yan Najeriya su kara hakuri, kada su ba Buhari lokaci ko wa’adin da zai kawar da matsalar tsaro a kasar nan.

“Ba Najeriya kadai ce kasar da ke fama da matsalar tsaro ba. Abin ya ma zama ruwan-dare, ya game duniya. Hatta manyan kasashe na duniya na fama da wannan matsala.”

Sace yara 344 da aka yi a Kankara Jihar Katsina, da kuma sace wasu 80 a Katsina din, a ranar da aka damka wadanda aka kubutar daga masu garkuwa, ya kara dagula harkar tsaro a kasar nan, wadda ta kara gigita duniya, a lokacin da Boko Haram su ka yi wa manoma 43 yankan-rago a Zabarmari, Jihar Barno.

Share.

game da Author