RANAR KANJAMAU TA DUNIYA: Za a samu karancin kudaden da ake kashe wa Kanjamau saboda Korona

0

Kungiya mai zaman kanta AIDs Healthcare Foundation (AHF), ta ce akwai yiwuwar samun karancin kudaden da ake kashe wa Kanjamau saboda Korona.

Kungiyar AHF Kungiya ce dake aiki a kasashe 22 har da Najeriya kuma ta sanar da haka ne a ranar Talata ranar cutar kanjamau ta duniya.

AHF ta ce duk shekara duniya na samu bashin dala biliyan 6 a cikin kudaden da ake bukata wajen yaki da cutar.

An tsaida ranar 1 ga Disamba domin tunawa da wadanda suka mutu ko suke fama da kanjamau a duniya.

Sannan ana amfani da wannan rana domin kara fadakar da mutane game da cutar tare da karfafa giwiwar mutane wajen yin gwajin cutar.

Sakamakon binciken da Hukumar UNAIDS ta yi, ya nuna cewa mutum miliyan 38 na dauke da kwayoyin cutar kanjamau a duniya.

Sakamakon binciken ya kara nuna cewa an samu karuwan mutum miliyan 1.7 da suka kamu sannan mutum 690,000 sun mutu a dalilin fama da cutar a duniya a shekarar 2019.

A wannan shekara mutum 45,000 sun mutu a Najeriya.

Matsalar rashin kudi

A wani hira da ya yi da PREMIUM TIMES shugaban hukumar dakile yaduwar cutar kanjamau ta ƙasa NACA Gambo Aliyu ya ce gwamnati za ta bude asusu domin Tara kudaden da za a siya maganin kanjamau da su.

Aliyu ya ce kudaden da za a tara a asusun zai isa a siyo maganin cutar wa akalla kashi 40% dake fama da cutar a kasar nan.

Ya Kuma ce gwamnati za ta karkato da hankalin gwamnatocin jiha domin zama Kan gaba wajen yaki da cutar a kasar nan.

Share.

game da Author