Wata sanarwa da ta fito daga Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo, ta ce za a fara raba wa direbobi da ‘yan dako naira 30,000 kowanen su, domin tallafa masu da abin rage raɗaɗin ƙuncin da annobar korona ta haddasa wa masu karamin ƙarfi a kasar nan.
Za a raba masu kudaden a karkashin Shirin Hana Tattalin Arzikin Masu Karamin Karfi Durkushewa, wanda tuni aka fara amfanar da wasu masu kananan kasuwanci bisa tsarin MSME.
A yanzu kuma shirin ya karkato kan direbobin taksi, na bas-bas, matuka Keke-Napep, ‘yan acaba da masu dako a kaauwanni, wato masu tura ‘barrow’.
Sanarwar wadda Kakakin Yada Labarai na Mataimakin Shugaban Kasa, Laola Akande ya sa wa hannu, ta ce kowane direba ya je ya yi rajista da kungiyar su.
Irin wadannan kungiyoyin sun hada da NURTW da sauran kungiyon ‘yan acaba da na direbobin Keke-Napep.
A cikin sanarwar, Akande ya ce zuwa karshen Nowamba an raba wa masu kananan sana’o’i su 59,000 kudaden tallafi. Ya ce sun fito ne daga jihohi 24 da su ka hada da FCT Abuja, Lagos, Ekiti, Bauchi, Anambra, Abia, Rivers, Filato, Delta da Taraba.
Sauran jihohin su ne Adamawa, Bayelsa, Edo, Ogun, Katsina, Kebbi, Kogi, Kwara, Enugu da Ebonyi.
Sanarwar ta ce ana kan kokarin raba na sauran jihohin.
Dalla-dallar yadda aka raba wa masu karamin karfin jarin, sanarwar ta ce an raba wa mutum 180,196 kowanen su naira 30,000. An raba naira 50,000 ga kowane mutum ga mutane 27,353.
Ya ce kashi 2.6% na wadanda aka raba wa kudaden tallafin, duk mabukata ne “na musamman.” Akwai kuma kashi 42% na adadin wadanda mata ne.
A karkaahin Shirin Tallafin Direbobi dai za a raba naira 30,000 ga kowane, a cikin ‘yan taksi, acaba, Keke-Napep da ‘yan dako har su 4505.
Sai cikon rukuni na 3 na masu kananan sana’o’i su 4504 su ma da za a raba wa naira 30,000 kowanen su.
Discussion about this post