PDP ta yi kira ga INEC ta soke rajistar jam’iyyar APC

0

Jam’iyyar adawa ta PDP ta yi kira ga hukumar zabe, INEC ta soke rajistar jam’iyyar APC.

Kakakin jam’iyyar Kola Ologbondiyan, ya bayyana cewa tunda jam’iyyar APC ta rushe dukkan shugabannin ta na jihohi, kananan hukumomi da na mazabu ya nuna cewa jam’iyyar bata kenan.

” Muna kira ga hukumar zabe ta bayyana kujerun duka ‘yan APC ba kowa a kai, a sake zabe ko a baiwa wadanda suka zo na biyu a zabukan da ya kai su ga kujerun. Sannan kuma muna kira ga kowa da kowa ya maida APC rusasshiyar jam’iyya a yanzu.

” Yanzu tunda jam’iyyar APC ta zama rusasshiyar jam’iyya a kasar nan, muna kira ga hukumar zabe ta fara shirin gudanar da zabuka a kujerun ‘yan majalisu gaba daya, saboda bata da kwamitin gudanar wa a yanzu kamar yadda dokar kasa ta gindaya.

PREMIUM TIMES ta buga labarin rushe kwamitin gudanarwar jam’iyyar APC da suka hada da shugabannin jam’iyyar na jihohi, kananan hukumomi da na mazabun kasar nan baki daya.

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai ne ya bayyana haka ga manema labarai bayan tashi daga taro a Abuja.

Ya ce rushewar ta shafi shugabannin jam’iyya na rumfunan zabe, na mazabu, na Kananan Hukumomi da na jiha da na shiyya baki daya.

Kamar yadda PREMIUM TIMES ta yi zato, APC ta kuma kara wa Shugaban Riko Mai Mala Buni karin wa’adin karin wasu watanni shida.

Sannan kuma an yi fata-fata dai tsohon mataimakin APC na Kudu maso Kudu, Williad Eta.

“Majalisar Zartaswa ta APC ya kuma amince da yin karin wa’adin wasu watanni shida. A da wa’adin Shugaban Riko zai kare a ranar 25 Ga Disamba, 2020. Amma yanzu zai ci gaba, zuwa watan Yuni, 2021 30 Ga Wata.

“Majalisar Zartaswar APC ta amince da korar Hilliard Eta, saboda ya bijire wa umarnin uwar jam’iyya, inda ya ci gaba da karar da ya kai, duk kuwa da cewa uwar jam’iyya ta ce duk wani wanda ya kai kara, to ya janye a yi maslaha”.

Eta, wanda dan ga-ni-kashe-in Adams Oshiomhole ne, ya kai kara bayan rushe su da aka yi, alhali Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi wadanda su su ka kai kara kotu, to su yayyafa wa zukatan su ruwa, su janye.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin jawabin da Buhari ya yi a wurin taron, inda ya nemi a hada kai, a jajirce kuma a yi sadaukarwa domin a kare martabar jam’iyya.

Share.

game da Author