Ni ma na koma APC kawai – Inji ‘Small Alhaji’

0

Dan majalisar Tarayya da ke wakiltar shiyyar Idanre/Ifedore, Tajuddeen Adefisoye, ya canja sheka daga SDP zuwa APC.

Dama dai Adefisoye wanda aka fi sani da ‘Small Alhaji’ shine dan majalisa daya tilo dan jam’iyyar SDP dake majalisar Tarayya.

A wasikar canja sheka da ya karanta a zauren majalisar tarayya, kakakin Majalisar Femi Gbajabiamila ya ce Adefisoye ya ce baya ga zaman kadaici da ya dame shi, jam’iyyar SDP har yanzu a cukuikuye ta ke inda har yanzu ba a san shugabanta ba.

Share.

game da Author