Isah Suleiman, dan asalin unguwar Panshekara, jam’iyyar har Kano ya bayyana cewa shi dama can burinsa shine Allah ya hada shi da wata baturiya ya aure ta.
Idan ba a manta ba a ranar Lahadi ne Isah, wanda mai aski ne ya auri Janine Sanchez yar kasar Amurka a birnin Kano.
Wannan bikin aure ya samu halartar mutane da dama da ya hada da sanata Shehu Sani.
Yadda Muka Hadu Da Janine
Isah ya ce ya hadu da Janine ne a shafin sada zumunta ta Instagram. Daga nan ne fa Isah, ya ce suka fara tattaunawa har soyayya ya shiga tsakanin su.
” Bayan soyayyar mu ta yi karfi matuka sai na umarce ta ta zo Kano mu yi aure, Janine kuma ta yarda.”
Janine ta na da ƴaƴa biyu tare da tsohon mijin ta ba’amurke.
Ta kara da cewa ba za ta zauna a Najeriya ba. Za ta koma can ƙasar ta tare da mijin ta Isah su ci gaba da zama.
Iyayen Isa da ƴqn uwan sa sun taya ɗan su murna sannan sun bishi da addu’o’in Allah ya sa an yi a sa’a.
A karshe Isah ya ce burin sa a ce yau ya haifi ɗa ko ƴaƴa da baturiya, ga shi yanzu burin sa ya kusa cika.
Discussion about this post