A wata wasika da jami’ar Amurka ta rubuta wa PREMIUM TIMES da gwamnatin jihar Kano kan ko da gaske ne duk da sanin cewa an taba ganin Gwamnan Kano a 2018 yana karbar cin hanci karara daga ƴan kwangila jami’ar ta nada shi Farfesa.
Mahukuntan jami’ar ECU dake Amurka sun karyata cewa wai jami’ar ta nada Ganduje farfesa na musamman a jami’ar.
Sannan kuma ta aika wa shi kansa gwamnan cewa jami’ar bata nada shi farfesa ba sannan ba, wanda ma ya yi masa albishir da haka, ya kantara masa karya ne.
An ruwaito labarin yadda kakakin gwamna Kano ya shaida wa manema labarai cewa wai jami’ar Amurka ta nada Ganduje Farfesa.
An ce Jami’ar East Carolina University dake kasar Amurka ta nada gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje farfesa na jeka ka dawo a jami’ar.
An kuma ruwaito cewa Ganduje zai rika zuwa jami’ar yana yin musayan ra’ayi da karantar da dalibai masu karatun PHD, kananan malamai da baiwa sashen bincike kan al’muran kasashen waje shawara.
Idan ba a manta ba, an taba ganin gwamna Ganduje a wani bidiyo da aka dauka a asirci ya na karbar cin hancin daloli daga hannu wani ɗan kwangila ya dannawa a cikin aljihan jamfar sa.
Mawallafin jaridar Daily Nigerian, Jaafar Jaafar, ne ya bankado wannan bidiyo, wanda BBC da Premium Times suka tabbatar da asali da sahihancin sa.
Duk da Jaafar ya bayyana a gaban majalisar jihar domin kare kansa da tabbatar da haka, gwamna Ganduje ya nemi a dakatar da sauraren wannan badakala bisa ga kariyar da yake mora a matsayin sa na gwamna.
Kotu ta amince da haka, ta dakatar da cigaba da binciken.
Ganduje da makarraban sa basu iya karyata wannan bidiyo har zuwa lokacin da aka dakatar da wannan bincike a majalisar jihar.