Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Sadiya Farouq, ta bayyana alhinin ta kan kisan gillar da ‘yan ta’adda su ka yi wa manoma 43 a Jihar Borno, ta na mai bayyana kisan da cewa mummunan aiki ne da kuma rashin tausayi.
Aƙala manoma 43 aka yi wa mummunan kisa a ƙauyen Zabarmari da ke cikin Ƙaramar Hukumar Jere ta Jihar Borno a ranar Asabar a fadamun shinkafa, yayin da aka bada rahoton cewar mutum shida sun ji rauni. An bayyana cewa kusan dukkan su ‘yan Jihar Sokoto ne da su ka je cirani a fadamun shinkafa.
Sadiya ta yi magana ne a cikin wata takardar saƙon ta’aziyya da ta aika wa da gwamnatin Jihar Borno.
A takardar, ministar ta yi wa al’ummar jihohin Borno da Sokoto da gwamnatocin jihohin ta’aziyyar abin da ya faru.
Ta ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya za ta yi dukkan abin da za ta iya wajen kawo ƙarshen hare-haren da masu tsattsauran ra’ayi ke kaiwa, kuma ta roƙi Allah da ya kare jama’a.
A dalilin wannan kisa da aka yi wa manoman Zabarmari, Majalisar Dattawa ta sake yin kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke shugabannin tsaron kasar nan na soja.
A wani zama da su ka yi a ranar Talata biyo bayan mummunan kisan yankan rago da aka yi wa manoma su 43, sanatocin Najeriya sun nemi ya cire shugabannin tsaron kasar nan, ya maye gurbin su da wadanda su ka san abin da su ke kuma masu babbin dabarun kakkabe Boko Haram.
An binne su ranar inda kuma Shugaban Majalisar Dattawa ya ja zugar manyan da su ke rike da madafun iko, domin mika ta’aziyya, jaje da kuma alhini.
Wancan ne karo ma uku da Majalisar Dattawa ta roki Buhari ya cire su Buratai da sauran manyan hafsoshin tsaro.
Sanata Kashim Shettima ne ya fara bude wutar rokon Buhari ya cire shugabannin tsaron kasar nan.
Daga nan aka bar kowa ya yi na shi bayani.
Discussion about this post