A ranar Laraba Majalisar Tarayya ta jingine batun gayyatar da ta yi wa Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana a gaban ta, domin yin bayani da amsa tambayoyi a kan matsalar tsaro a fadin kasar nan.
Majalisar ta gayyaci Buhari biyo bayan yankan ragon da ‘yan Boko Haram su ka yi wa manoma 43 a kauyen Zabarmari, cikin Karamar Hukumar Jere, a jihar Barno.
A ranar da Majalisar Tarayya ta ce za ta gayyaci Buhari ya je ya yi bayani, ita kuwa Majalisar Dattawa kira ta sake yi a karo na uku cikin watanni shida ga Buhari ya tsige shugabannin fannonin tsaron Najeriya.
Majalisar Tarayya dai ta jingine batun gayyatar Buhari ta hanyar tsallake batun a ranar Laraba, aka ki karanta shi, ballantana a aza ranar da Buhari zai bayyana.
Hakan da su ka yi, ya gaskata nazarin musamman da PREMIUM TIMES ta yi, wanda ta bugi kirjin cewa Buhari ba zai iya zuwa ya yi bayanin ba, duk kuwa da Fadar Shugaban Kasa ta ce zai amsa gayyatar.
Alamomin Buhari ba zai je Malajisa ba sun fara fitowa tun a ranar Talata, inda bayan Gwamnonin APC sun yi wata ganawa da Buhari cikin dare, su ka roke shi kada ya amsa gayyatar Majalisar Tarayya.
Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa sun shaida wa Buhari idan ya amsa gayyatar, to gwamnoni su ma za su bani su lalace wajen yawan gayyatar da ‘yan majalisar jiha za su rika yi masu.
Dama kuma a ranar Laraba kakocin watsa labarai sun ruwaito Ministan Shari’a Abubakar Malami na cewa Majalisar Tarayya ba ta da hurumin gayyatar Shugaban Kasa domin ya yi mata bayani a kan abin da ya shafi matsalar tsaro.
Bulalar Majalisa, Mohammed Monguno ya bayyana wa manema labarai cewa sun gano wata makarkashiya mambobin PDP su ka shirya domin su kunyata Buhari idan har ya yi giringishin bayyana a gaban su.
Kiri-kiri Hon. Ado Doguwa da Kakakin Majalisa Femi Gbajabiamila su ka tsallake batun kira ko gayyatar Buhari ba su tayar da zancen a ranar Laraba ba.