Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya ce duk wani dan siyasa ko daga wace jam’iyya, ya daina hauragiyar kokawar neman mulkin 2023 tun yanzu, a tsaya a fuskanci matsalar tsaro tukunna.
Saraki ya bada wannan shawara, ranar Laraba a Abuja, lokacin da ya ke kaddamar da Kwamitin Sasanta Rigingimun Jam’iyyar PDP.
“Dan siyasa na da ‘yancin fitowa neman mukami, amma maganar gaskiya yanzu da mu ke gaganiyar fama da matsalar tsaro, ba lokaci ne ne fita farautar mukamin siyasa ko mulki a 2023 ba.”
Saraki wanda shi ne Shugaban Kwamitin Sasanta Rigingimun PDP, ya ce abin da ke gaban su a yanzu shi ne yadda za a sake hada kan al’ummar kasar nan, samar da zaman lafiya, sake gina kasa da kuma kayar da wadanda su ka karbi mulki amma su ke jefa kasar nan cikin halin da aka rasa yadda za a fitar da ita daga kangin da su ka jefa ta, har su ke kokarin tarwatsa ta.
“Duk wani dan siyasar da bai damu da halin da kasar nan me ke ciki ba, ya kama gaganiyar neman mulki, to bai cancanci zabe a mukamin da ya ke hankoron samu ba.
“Mu a yanzu mun yi amanna cewa babu wani abu da ya fi wanzuwa da zamantakewar dorewar Najeriya a dunkule ba.” Inji Ssraki.
Saraki ya kara da cewa nasarar PDP ce kadai Najeriya ke bukata a yanzu domin kasar nan a kasance dunkulalliya marar bambancin da aka jefa ta haka kawai da rana tsaka.
Ya yi alkwarin cewa ‘yan kwamitin sa za su yi bakin iyawar su, domin ganin sun yi amfani da basirar su wajen dinke duk wata baraka da ke tattare da jam’iyyar PDP.
Ya ce tuni kwamitin na sa ya fara aiki tun ma kafin a rantsar da shi. Domin ya fara tuntubar wasu da kwamitin ya fahimci akwai bukatar ya tuntube su da gaggawa.
Sauran mambobin kwamitin sun hada da Anyim Pious Anyim, Ibrahim Shema, Liyel Imoke, Ibrahim Dankwambo da Mulikat Akande-Adeola.
Discussion about this post