A karshen taron da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi da gwamnonin Najeriya su 36, a ranar Talata, ya umarce su da su yi aiki kafada-da-kafada tare da sarakunan gargajiya da sauran shugabannin al’umma.
Buhari ya ce yin hakan zai samar da yanayin da za a rika samun bayanai mabuyar batagari, ta yadda za a rika taimaka wa jami’an tsaro a kokarin dakile ta’addanci da sauran hare-haren ‘yan bindiga a kasar nan.
Yayin da Buhari ya saurari rahotannin matsalar tsaro a bakin gwamna daya daga kowace shiyya, ya tunatar da su cewa a shekarun baya da nisa, duk jama’ar da su ka ga bakon-ido a cikin yankin su, to garzaya su ke yi su sanar da hukumar tsaron yankin.
“Amma yanzu yankin Afrika ta Yamma babu sauran zaman lafiya, tun bayan kifar da gwamnatin Mu’amar Ghadafi ta Libya, inda daga nan ne aka rika shigo mana da muggan makamai da kuma fantsamar muggan mahara cikin kasar nan.
“Ya zama dole gwamnoni su rika aiki tare da sarakunan gargajiya domin samun bayanai na sirri, wadanda za a bi a dakile hare-haren Boko Haram da ‘yan bindiga da sauran su.”
Buhari ya ce gwamnatin sa ta yi kokari wajen samar da tsaro a Arewa maso Gabas da Kudu maso Kudu. Amma har yanzu matsalar rashin tsaro a Kudu maso Kudu ta na matukar damun sa.
“A kullum ina samun rahoton matsalar fasa bututun mai da masu kafa kananan wuraren tace danyen mai da su ke sata. Tilas ku tashi tsaye ku kakkabe wadannan ‘yan iska, ku yi maganin su.”
Da ya ke magana a kan matsalar masu garkuwa da mutane, Buhari ya ce gwamnatin sa za ta kara himma wajen tura sojojin cikin dazuka, domin su shafe su daga doron kasa.
“Batun rufe kan iyaka kuwa dama an yi ne har da dalilin ana shigo mana da makamai da muggan kwayoyi. Amma yanzu tunda kasashe makwauta sun dauki darasi daga rufe kan iyakokin da Najeriya ta yi, to mu na tunanin sake bude kan iyaka nan ba da dadewa ba.”
Buhari ya tabbatar wa sojojin Najeriya cewa za su samu dukkan goyon bayan da su ke bukata domin su kakkabe muggan masu laifi a kasar nan.
“Ba na son bada labarin irin motocin da muka sai wa sojoji domin yin sintiri, amma dai mun sai wa sojoji motocin sintiri da kayan yaki, wadanda yanzu haka ana nan ana koyar da zaratan sojojin da za su rika koyar da wadanda za a koya wa yin amfani da su.
Buhari ya yi magana kan yadda batagari su ka maida zanga-zangar #EndSARS zuwa mummunar tarzoma. Kuma ya yi magana kan gidan talbijin na CNN da ya ce bai yi adalci wajen bada rahoton abin da ya faru a tirmitsitsin zanga-zanga a Lekki ba.
Yayin da Buhari ya nuna cewa bai ji dadin rahoton CNN ba, ya karkare da cewa daga yanzu ba za a sake barin batagari su maida zanga-zanga zuwa tarzoma ba.