Mata manoma sun jibge fartanya da magurbi a gidan tarihi, sun bukaci kayan noma na zamani

0

Mambobin Kungiyar Kananan Manoma Mata ta Najeriya (SWOFAN), sun yi tattaki har Hedikwatar Gidan Adana Kayan Tarihi ta Kasa da ke Abuja, inda su ka jibge fartanya da magirbi, su ka bayyana wa gwamnati cewa sun gaji da wahalar noma da kayan noma na gargajiya.

Da ta ke magana a madadin sauran matan, Shugabar Kungiyar Kananan Mata Manoma ta Kasa, Mary Afan, ta ce sun gaji da dukawa shekara da shekaru su na wahalar kartar noma da fartanya. Ta ce su na bukatar a raba masu kayan noma na zamani, wadanda ke samar da amfanin gona a saukake.

“Mun zo a yau domin mu jibge fartanya da magurbi da garmunan noman hannu. Saboda mun san nan ne gidan adana kayan tarihi. Nan gaba ‘ya’yan mu da jikokin mu idan su ka taso, za su iya kawo ziyara, domin su ka irin kayan noman da kakannin su su ka rika amfani da su wajen noma abincin ciyar da kan su da kasa baki daya, amma a wahalce.

“Wannan rana ce mai muhimmanci a wurin mu, domin mun yi ritaya daga aikin wahalar noma da fartanya, magirbi da garma.

“Yawan al’ummar Najeriya ya yi karuwar da noma da fartanya ba zai iya ciyar da kasa ba, tilas sai an koma yin amfani da kayan noman zamani.

“Noman fartanya ko garma noman wahala ne. Ga shi ba a iya noma abin kirki kuma na a iya noma makekiyar gona a cikin kankanin lokaci. Mu na shan bakar wahala kafin mu noma dan abin da bai taka kara ya karya ba.

“Noman fartanya da garma noman wahala ne, sannan ya na nukurkusar da jiki ya tsufar da mutum da wuri. Kuma a karshe ba ka iya noma abin kirki.”

Ta yi kira gwamnati ta samar wa mata kayan noma na zamani, wanda za su rika aiki mai yawa a rana daya, sannan kuma su rika noma maka-makan gonaki, ta yadda za su rika wadata kasa d abinci.

Daraktar Samar Walwala da Jin Dadin Mata ta Gundumar FCT Abuja, Agnes Hart, ta jinjina wa matan, ta na mai cewa hakkin da ya rataya a kan gwamnati ne ta samar wa mata kayan noma na zamani, wadanda ake gudanar da noma a saukake ta hanyar amfani da su.

“A gaskiya mun gaji da ganin mace rike da fartanya ko garma ta duka a cikin gona, ta na ta kartar noman da ba zai iya wadata kan ta da kasa baki daya ba.

” Wajibi ne a rika wadata mata manoma da kayan noma na zamani, wadattacen takin da zai bunkasa amfanin gonakin su.” Inji Afan.

Share.

game da Author