Maryam Umar, ta lashe gasar rubutun gajerun labarai ta mata zalla wanda BBC Hausa ke shiryawa duk shekara.
Labarin ‘Rai Da Cuta’ wanda Maryam Umar ta shiga gasar dashi ya duba yadda mutane ba su yarda da cutar korona ba, cutar da ta zama annoba a duniya.
Tauraruwar labarin mace ce mai juna biyu da mijinta ya kamu da cutar korona amma ya ƙi kai ta asibiti har ita ma ta kwashi cutar.
Mijin nata ya kulle ta a ɗaki har ta kusa rasa ranta sannan jaririn da ke cikinta ya mutu.
Maryam ta samu kyautar $2000.
A hira da tayi da PREMIUM TIMES HAUSA, Maryam tace wannan shine karo na uku da ta shiga wannan gasa amma sai a wannan karon Allah ya sa rubutunta ya yi zarra.
Maryam dalibar Jami’ar Usman Danfodiyo ne kuma mazauniyar jihar Sokoto.
Wanda ta zo na biyu, Surayya Yahaya ta shiga gasar da labarinta mai suna ‘Numfashin Siyasa’. Numfashin Siyasa labari ne kan wata matashiya da ta yi ƙoƙarin ceto al’umar ƙauyensu ta hanyar shiga siyasa.
Sai dai al’umarta ba ta shirya morar shugabanci daga hannun mace ba don haka sai ta juya mata baya.
A gwagwarmaryar siyasarta, tauraruwar labarin ta rasa iyayenta sannan ta fuskanci tsangwama da wulaƙanci daga mutanen ƙauyenta.
Wanda ta zo na uku a gasar, Rufaida Umar ‘yar asalin jihar Kano ce kuma tayi wa labarin ta suna ‘Farar kafa’.
Wannan labari ne kan wata wadda yarda da camfi ya jefa ta a cikin mawuyacin hali.
Bayan aurenta mijinta ya yi ta gamuwa da jarrabawa iri-iri kuma ya camfa cewa tana da farar ƙafa shi ya sa waɗannan iftila’i ke hawa kansa.
Rahama ta sha tsangwama dalilin haka kuma aka yi mata laƙabi da mai farar ƙafa.
Rufaida na da aure da ‘ya’ya biyu sannan Daliba ce a Kwalejin koyan aikin Malunta, FCE dake Kano.
Tace wannan shine karo na biyu da take shiga gasar Hikayata.
Anyi bukin karrama gwarazan a Abuja ranar Juma’a, 4 ga Disamba.