Malejin tsadar rayuwa a Najeriya ya kara cillawa sama watanni 14 a jere

0

Hukumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa, wato NBS,ta ce kuncin rayuwa a Najeriya ya karu da kashi 14.89, a watan Nuwamba, idan aka kwatanta da yadda ya karu a watan Oktoba daga watan Satumba.

A watan Nuwamba da ya gabata dai NBS ta ce kuncin rayuwa ya karu sakamakon masifar tsadar kayan abinci da kayan masarufi daga kashi 17.38 a cikin Oktoba, zuwa 18.30 a cikin Nuwamba.

Ya zuwa watan Oktoba da ya gabata dai kididdigar NBS, wadda hukuma ce ta gwamnatin tarayya, ta ce kuncin rayuwa ya rike wuta tsawon watanni 30 a jere malejin sa bai sauka kasa ba.

An danganta tsadar rayuwar da matsin tattalin arziki, rufe kan iyakoki da gwamnatin Buhari ta yi, tashin farashin kayan masarufi da kuma hare-haren ‘yan bindiga da Boko Haram, wadanda ke hana manoma zuwa gonaki su kwashe amfanin gonar da su ka noma.

Rahoton da NBS ta buga a ranar Talata, a shafin ta intanet, ya nuna cewa kaya sun kara farashi da kashi 0.66, wato kashi 14.23 kenan idan aka kwatanta da watan Oktoba.

Dama a baya dai kulle kan iyakoki ya haifar da mummunar hauhawar farashi. To sai kuma iska ya tarad da kaba na rawa, inda cutar korona ta karasa durkusar da tattalin arzikin Najeriya.

Kashe-kashen Boko Haram da hare-haren masu garkuwa ya hana manoma zuwa gonaki debe amfanin gonar da su ka noma.

Cikin watan Nuwamba Boko Haram sun yi wa manoman shinkafa yankan-rago a Zabarmari, cikin jihar Barno.

Kayan abinci da su ka hada da burodi, sarelak, tumatir, doya, albasa, nama, kifi, kayan marmari, kayan miya da mai duk sun tsula tsada.

Cikin Nuwamba an samu hauhawar farashi a jihohin Kogi, Bauchi, Zamfara, Sokoto, Ebonyi.

Haka ma a jihohin Osun da Cross River duk an samu hauhawar farashin kayan abinci da na masarufi a jihohin.

A cikin watan Oktoba ma sai da Hukumar Kididdigar Alkalumman Bayanai ta Kasa (NBS), ta bayyana tsadar rayuwa a Najeriya ta yi tsananin da watanni 30 baya ba a taba fuskanta ba.

NBS, wato ‘National Bureau of Statistics’, ta ce farashin tsadar rayuwa ya yi sama zuwa kashi 14.3 bisa 100 a cikin Oktoba, abin da aka rabu da gani tsawon watanni 30 da su ka gabata.

Tsadar rayuwar ta karu daga watan Satumba, wanda tsananin ya tsaya kashi 13.71 a watan Satumba.

Tsakanin Satumba zuwa Oktoba an samu karin kashi 1.54. Hakan ya nuna rayuwa ta fi tsanani tsakanin watan Satumba zuwa Oktoba fiye da tsakanin watan Augusta zuwa Satumba.

Tsananin tsaurin rayuwa na ci gaba da ta’azzara ta hanyar hauhawan farashin kayan abinci da na masarufi, tun daga lokacin da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ya kulle kan iyakokin kasar nan, da nufin dakile fasa-kwauri, musamman na shinkafa.

Lamarin ya kara muni yayin da barkewar annobar korona ta tsayar da komai cak a Najeriya da ma duniya baki daya.

Saboda hakan ne ya har yau tattalin arziki bai kai ga farfadowa daka dukan da korona ya yi masa ba.

A cikin rahoton, an bayyana yadda farashin kayan abinci ya yi tashin-gwauron-zabo daga kashi 16.66 cikin Satumba, ya koka 17.38 cikin Oktoba, 2020.

Kayayyakin da su ka kara masifar tsada sun hada biredi, seralak, dankalin Turawa, doya, rogo, makani da gwaza, nama, kifi da man girke-girke.

Jihohin da su ka fuskanci tashin farashin komai sun hada Sokoto, Edo, Akwa Ibom, yayin da Oyo, Taraba da Jigawa ba su fuskanci hauwhawar farashi sosai ba.

Idan ba a manata ba, ranar I Ga Afrilu, 2019, an bayyana cewa Najeriya ce kasa ta 6 da ake fuskantar kuncin rayuwa a duniya

A ranar ce wani rahoto a wata jami’a ta Amurka ya bayyana yadda al’ummar Najeriya ke cikin kuncin rayuwa.

Wani rahoto na duniya da jami’ar Baltimore ta Amurka ta fitar ya bayyana cewa Najeriya ita ce kasa ta shida da al’ummarta ke fama da kuncin rayuwa.

Rahoton ya ce an yi amfani da wasu alkaluma da suka hada rashin ayyuakan yi da tashin farashin kayayyaki da kuma tsawwala kudin ruwa a lokacin neman rance a bankunan kasar.

Tuni dai masana tattalin arziki a Najeriya suka ce akwai kamshin gaskiya a wannan rahoto bisa la’akari da wasu abubuwa da ke faruwa a kasar.

Alhaji Shu’aibu Idris, masanin tattalin arziki ne a Najeriyar, ya shida wa BBC cewa, bisa la’akari da abubuwan da aka bayyana a cikin rahoton wadanda suka kai Najeriya ga wannan matsayi, akwai kamshin gaskiya.

Ya ce ‘ Idan aka duba irin kudin ruwan da bankunan Najeriya ke sanya wa masu kabar bashi, to a gaskiya a duk kasashen Afirka idan Najeriya ba ta zo ta daya ba, to ba za ta wuce na uku ba koshakka ba bu’.

Masanin tattalin arzikin, ya ce haka a bangaren rashin aikin yi kuwa, akwai kusan kaso 20 zuwa 27 na matasan kasar da ba su da aikin yi.

Alhaji Shu’aibu, ya ce idan aka yi nazari a kan wadannan matsaloli ma kadai a Najeriya, to za a gane cewa ko shakka ba bu al’ummar kasar na cikin kunci rayuwa a kowanne lokaci.

Wani kwararre kuma fitacce a kan harkokin tattalin arziki na duniya, Steve Hankens daga Amurkar, shi ne ya wallafa rahoton.

Rahoton dai ya bayyana kasar Venezuela a matsayin kasa ta farko da akafi shaida kuncin rayuwa sannan Argentina sai Iran, sannan Brazil wadda ta zo ta hudu, sai Turkey ta biyar, sannan kuma Najeriya da ta zo ta shida.

Share.

game da Author