Yayin da Majalisar Tarayya ta amince da Kasafin 2021 na naira tiriliyan 13.06, ta kuma yarda da awon sikelin kasafin a kan farashin gangar danyen man fetur da 40.
A wani zama na musamman na karshen shekara, mambobin majalisar a ranar Litinin, sun amince da fara ware naira bilyan 496 ga wadansu hukumomi da su ka hada da Malalisar Tarayya da Hukumar Zabe Ta Kasa (INEC), a matsayin abin da za a fara cirewa daga kasafin na 2021.
Sannan kuma sun amince da cewa za a kashe naira tiriliyan 3.3 na kasafin kudin wajen biyan basussuka, sai kuma naira tiriliyan 4.1 da za a kashe wajen gudanar da manyan ayyuka.
PREMIUM TIMES ta bada lllabarin yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana yadda aka cimma shata hasashen kashe naira tiriliyan 13.08 a Kasafin Najeriya na 2021.
Sai dai a yanzu kuma saboda lalacewar darajar naira, kasafin na 2021 ya koma a kan duk dalar Amurka 1 kan naira 500.
Wannan ne karo na shida da Buhari ya gabatar da kashe kasafin shekara-shekara tun bayan hawan sa mulki a 2015.
Ya gabatar da na 2016, 2017, 2018, 2019 da kuma na 2020 a shekarun baya a jere.
Kasafin wanda aka rada wa suna, “Kasafin Fardado Da Tattalin Arziki”, Buhari ya ce an tsara shi a matsayin sharar-hanyar kudirin gwamnatin sa na bunkasa tattalin arzikin Najeriya a karkashin Shirin NDP 2021 – 2025.
Ya ce an kintacen farashin gangar danyen man fetur a kan dala 40, wanda akan wannan ma’auni ne aka yi kasafin dungurugum.
Sannan ya kara da cewa an sake auna ma’aunin a kan kowace dala daya daidai da naira 376.
Ya ce an yi kasafin a bisa hasashen za a rika hako danyen mai ganga milyan 1.86 a kowace rana.
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kintacen cewa Najeriya za ta tara kudaden haraji har naira tiriliyan 8.433 a cikin 2021.
Ya ce daga cikin wadannan kudaden za a kashe naira tiriliyan tiriliyan 7.886 wajen Kasafin 2021. Amma daga cikin akwai kudaden agaji da tallafin da manyan cibiyoyi na duniya kan bayar, har naira bilyan 354.85.
Sannan kuma akwai kudaden shiga da za a karba a hukumomin gwamnatin tarayya har 60.
Buhari ya ce ana kintacen tara kudin shiga daga ribar fetur har naira tiriliyan 2.01. Sauran kudaden shigar da ba na fetur ba kuwa, ana sa ran za a tara naira tiriliyan 1.49.
PREMIUM TIMES ta buga labarain cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kintacen cewa Najeriya za ta tara kudaden haraji har naira tiriliyan 8.433 a cikin 2021.
Ya ce daga cikin wadannan kudaden za a kashe naira tiriliyan tiriliyan 7.886 wajen Kasafin 2021. Amma daga cikin akwai kudaden agaji da tallafin da manyan cibiyoyi na duniya kan bayar, har naira bilyan 354.85.
Sannan kuma akwai kudaden shiga da za a karba a hukumomin gwamnatin tarayya har 60.
Buhari ya ce ana kintacen tara kudin shiga daga ribar fetur har naira tiriliyan 2.01. Sauran kudaden shigar da ba na fetur ba kuwa, ana sa ran za a tara naira tiriliyan 1.49.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana wa Sanatoci da Mambobin Majalisar Tarayya cewa Ministar Harkokin Kudade Da Tsare-tsaren Tattalin Arziki ce za ta yi wa Majalisa bayani dalla-dalla na abin da kowane bangaren kasafin ya kunsa.
Buhari ya fadi haka ne da ya ke gabatar da kasafin kudi na 2021 a zauren majalisar Tarayya ranar Alhamis.
“Mun gabatar da Kasafin 2021 a daidai lokacin da duniya ke fama da gaganiyar annobar cutar korona, wadda sanadiyyar hakan ta haifar da karyewar farashin danyen man fetur, abin da hakan kuma ya kawo cikas ga tattalin arziki.
“Tattalin arzikin Najeriya ya samu tawaya domin karin tattalin arzikin cikin gida (GDP) ya ragu da kashi 6.1 a watanni Afrilu, Mayu, Yuni da Yuli na shekarar 2020. Amma duk da haka, karfin tattalin arzikin Najeriya ya fi na sauran manyan kasashen duniya da kasashe masu tasowa karfin jure dadin kibiyar matsalar da annobar korona ta haifar a duniya.
Daga nan sai ya kara da cewa Gwamnati ta kirkiro aikin-karfi ga matasa 774,000 a fadin kananan hukumomi 774 na kasar nan domin rage kuncin rayuwa.
“ Mun kuma kirkiro Shirin Tallafa wa matasa da naira bilyan 75. Tuni ma har an saka naira bilyan 25 daga cikin kudaden Kasafin 2021 domin a fara yin somin-tabi sa su.
Za mu ciwo wa Kasafin 2021 bashin naira tiriliyan 4.28 -Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa za a samu gibin naira tiriliyan 4.28 a Kasafin 2021.
Da ya ke bayanin yadda za a cike gibin, Buhari ya shaida wa gamayyar majalisin Dattawa da Mambobin Tarayya cewa bashi za a ciwo domin a yi wa al’umma ayyukan raya kasa, saboda kudaden shigar da Najeriya ta yi hasashen tarawa, ko kadan ba za su isa a yi manyan ayyukan da su ka kamata a yi da su ba.
Buhari ya ce cikin 2021 za a kashe naira bilyan 501.19 wajen biyan kudaden fanshon tsoffin ma’aikata.
Ya ce za a kashe naira tiriliyan 3.124 wajen biyan basussukan da su ka yi wa Najeriya katutu.
Hukumar Bunkasa Yankin Neja-Delta (NDDC) za ta samu naira bilyan 63.51. Hukumar Farfado da Yankin Arewa maso Gabas za ta samu naira bilyan 29.70, sai Hukumar Bunkasa Ilmi a Matakin Farko (UBE) ta za samu naira bilyan 70.
Za a bai wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) naira bilyan 40, sai Majalisun Dattawa da ta Tarayya naira bilyan 120.
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana yadda aka cimma shata hasashen kashe naira tiriliyan 13.08 a Kasafin Najeriya na 2021.