Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterrez, ya yi kira da a gaggauta sakin daliban Katsina da aka yi garkuwa da su.
Guterrez ya yi bayanin a cikin wata takarda da Jami’ar Yada Labarai ta UN, Staphene Dujarric ta fitar a ranar Litinin.
“Ina kira da a gaggauta saki daliban Sakandaren Kiminiyya ta Gwamnati su sama da 300 da aka kama a Kankara, jihar Katsina a Najeriya.”
An fitar da sanarwar a birnin New a York na Amurka, inda hedikwatar UN din ta ke.
“Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya kara jaddada cewa kama daliban sakandare din da aka yi, ya saba da Yarjejiyar Majalisar Dinkin Duniya ta ‘Yancin Dan Adam, wadda ko da wasa ta haramta kama kananan yara.
Sannan kuma UN ta yi kira ga jami’an tsaron Najeriya su kokarta su kamo masu hannu a kama yaran 333, domin doka ta hukunta su.
Ya kara jaddada goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya ga Najeriya wajen kokarin kasar ga dakile ta’addanci da mahara daban-daban da su ka addabi kasar.
Hukumar UNICEF ita ma ta nuna matukar jimamin kama yaran da aka yi.
Cikin wata takarda da Daraktar UNICEF mai kula da Afrika ta Yamma da ta Tsakiya, Marie-Pierre Poinier ta fitar, ta ce na ta taya dukkan iyayen yaran alhinin bakin cikin rabuwa da yaran na su a cikin wannan mawuyacin hali.
Ya yi kira a gaggauta ceto yaran, tare da cewa ya kamata karamin duk inda ya ke a duniya, to ya kasance ya na zaune inda zai ji tabbar ran za a tsare ya ke, ba tare da wata barazana ba.
Discussion about this post