Majalisar Dattawa ta amince da nadin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu zango na biyu.
Amincewar wadda su ka yi a ranar Talata, ta biyo bayan rahoton da Kwamitin Zabe na Majalisar Dattawa a karkashin shugabancin Sanata Kabiru Gaya ya mika wa Majalisar a makon da ya gabata.
Kwamitin Kabiru Gaya ya gayyaci Yakubu a ranar Alhamis domin sake tantance shi, bayan Buhari ya tura wa Majalisar Dattawa din wasikar bukatar amincewar su da sake nadin da ya yi wa Yukubu a karo ma biyu, bayan kammala zangon sa na farko a cikin Nuwamba. 2020.
Buhari ya nada Yakubu da farko a cikin Nuwamba, 2016 bayan kammala wa’adin Farfesa Attahiru Jega a karo na biyu.
Yakubu zai ci gaba da aikin sa na shugabancin INEC nan take.
Yayin da ya ke bayani, Sanata Gaya ya ce Yakubu ya cancanci ci gaba da rike INEC bisa la’akari da cewa ya yi rawar gani a zabukan baya da ya gudanar, ba ya da rajista ko goyon bayan wata jam:iyyar siyasa, kuma ba a taba rubuta takardar korafi a kan sa ko da guda daya ba, ballantana har a ce an kama shi sa wani laifi ko bangaranci.
Sanatoci sun rika mikewa daya bayan-daya su na yabon irin kokarin Yakubu.
A na sa jawabi yayin tantance shi, Yakubu ya ce to fa akwai aiki wurjanjan a wuyan INEC kafin zaben 2023.
“Akwai muhimman ayyuka har guda 1508 da INEC za ta gudanar nan da cikin kwanaki 814 kafin zaben 2023.
Ya roki a gina dankara-dankaran ofisoshin INEC a kowace jiha har da Abuja, kakkarfan ginin da gobara ba za ta iya lalata wurin adana takardun bayanan alkaluman kididdigar kuri’un zabe ba.