Majalisar Dattawa ta sake yin kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya kori shugabannin tsaron kasar nan na soja ya musanya su da sabbin jini.
A wani zama da su ka yi a ranar Talata biyo bayan mummunan kisan yankan rago da aka yi wa manoma su 43, sanatocin Najeriya sun nemi ya cire shugabannin tsaron kasar nan, ya maye gurbin su da wadanda su ka san abin da su ke kuma masu babbin dabarun kakkabe Boko Haram.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Boko Haram sun ka yi wa masu aikin noma su 43 yankan rago a kauyen Zabarmari, cikin Karamar Hukumar Jere ta jihar Barno.
An binne su ranar Lahadi inda kuma Shugaban Majalisar Dattawa ya ja zugar manyan da su ke rike da madafun iko, domin mika ta’aziyya, jaje da kuma alhini.
Wancan ne karo ma uku da Majalisar Dattawa ta roki Buhari ya cire su Buratai da sauran manyan hafsoshin tsaro.
Sanata Kashim Shettima ne ya fara bude wutar rokon Buhari ya cire shugabannin tsaron kasar nan.
Daga nan aka bar kowa ya yi na shi bayani.
Sanata Ali Ndume wanda ya yi magana kan shirin gwamnati na kama ‘yan Boko Haram ta na sakin su, shi ma ya goyi bayan a cire shugabannin tsaro na kasar nan.
Yayin da wasu ke cewa Buhari ya kokarta, amma akwai bukatar ya nunka wannan kokari da ya ke yi.
Sanata Baba Kaita ya ce Buhari Na kokari, sai dai kuma ya kara da bayani cewa a kafa kwamiti a gano yadda hukumomin tsaro ke yi da kudaden kudi Na shekara.
“Ya kamata Buhari ya sallame su haka nan. Sun ci na su rabon su na cin rabon wasu. Idan ma ba zai iya Kawar da su ba, to ya kafa kwamitin wakilai masu ba shi shawara. A can ma din za su rika ba shi shawarar.
Idan ba a manta ba majalisar tarayya, ita ma a zamanta ranar Talata ta sammaci ta aika wa Buhari ya bayyana a gabanta.
PREMIUM TIMES ta buga labarin da Ministan Yada Labaran Najeriya, Lai Mohammed ya dora laifin kasa shawo kan Boko Haram a kan rashin hadin kai da ya ce kasashen duniya ba su bai wa Najeriya.
Lai ya ce kasashen duniya ke tadiye kafafun Najeriya ta na kasa dakile ta’addanci.
Ministan Yada Labarai Lai Mohammed, ya ce kiri-kiri kuma da gangan manyan kasashen duniya ke kin sayar wa Najeriya manyan makaman da za ta yi amfani da su ta murkushe Boko Haram.
Lai ya yi wannan jawabi a ranar Litinin lokacin da ya kai ziyara ga Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai a Makurdi, babban birnin jihar.