Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa,Ovie Omo-Agege, ya bayyana cewa Majalisa ba ta da karfin ikon canjawa ko sauya kundin dokokin Najeriya.
Kakakin Yada Labarai na Mataimakin Shugaban Majalisa, mai suna Yomi Odunuga ne ya fito da wannan bayani, cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai.
Ya ce Omo-Agege ya yi furucin ne a lokacin da mambobin Kungiyar Alliance of Nigerian Patriots su ka kai masa ziyara a ofishin sa.
Mambobin sun kai ziyarar ce a karkashin shugaban su Umunna Orjiako.
Omo-Agege, wanda shi ne Shugaban Kwarya-kwaryan Kwamitin Sake Nazarin Kundin Tsarin Mulki, ya ce Majalisar Dattawa ba ta da hurumim sauya dokokin kasa.
Ya ce abin da kawai za su iya yi, shi ne su yi wa doka ko wasu ba’arin sassan doka kwaskwarima.
Daga nan sai ya buga misali da irin dimokradiyyar manyan kasashe, kamar Amurka, wadda a can aka kwafo tsarin dimokradiyyar Najeriya.
Sannan kuma ya buga misali da Sashe na 8 da na 9 daga kundin dokokin Najeriya, domin misalin sa ya kara karfi sosai.
Ya ce abin da kawai aka amince wa Majalisa yi a kan dokoki ko wata doka, shi ne yi wa wani sashe na ta kwaskwarima, amma ba sauya gundarin kundin kwansitushin gaba dayan sa ba, ko kuma cire wata doka a sauya ta da wata.
Daga nan sai ya yi kira ga masu neman a musanya ko a canja kundin tsarin mulki da su shiga gadan-gadan wajen yi wa dokoki kwaskwarima.
Discussion about this post