Daliban makaranta da yawa ne mahara dsuka yi warwason su a makarantar sakandaren dake Kankara jihar Katsina.
Wani mazaunin kankara ya bayyana cewa sai da maharan suka afka cikin garin Kankara amma kuma jami’an tsaro sun fatattake, daga nan ne suka dira makarantar sakandaren dake Kankara.
An ce maharan sun afka makarantar ne wajen misalin karfe 12 saura akan babura daga nan sai suka rika harbin bindiga ta ko ina babu kakkautawa domin tsorata masu gadin makarantar da daliban.
Wasu daliban sun arce cikin daji wasu kuma an yi awon gaba da su.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ya tabbatar da aukuwar wannan mummunar al’amari ya an mai cewa an ji ma wani dan sanda rauni a wannan arangama.
“An samu rahoton cewa wasu daga cikin daliban sun dawo makaranta a safiyar Asabar.”
Iyaye da dama sun yi tururuwa zuwa makarantar domin gano ‘ya’yan su, sai dai hukumar makarantar tace ana ci gaba da bincike domin gano wadanda maharan suka tafi dasu.