Mahara sun sace mata mai Jego a Gujungu

0

Mahara dauke da muggan makamai sun sace wata mata mai jego a garin Gujungu, dake karamar hukumar Taura, jihar Jigawa

Mazauna garin Gujungu sun shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa maharan sun afka wa kauyen cikin dare inda suka doshi gidan wani Basiru Inusa, suka dauke matar sa dake jego.

Audu Jinjiri, kakakin rundunar ‘yan sandan Jigawa ya tabbatar da aukuwar wannan al’amari, ya kuma kara da cewa sai bayan awa 8 da aukuwar abin sannan aka sanar da ‘yan sanda.

Share.

game da Author