Mahara sun bindige Sarkin Maharban Adamawa a dajin Kaduna

0

’Yan bindigar cikin dajin Kaduna sun bindige Sarkin Maharban Adamawa a wani gumurzu da su ka yi a cikin dajin.

Majiya a cikin iyalan sa, ta tabbatar da kisan da aka yi wa Sarkin Kungiyar Maharba na Jihar Adamawa, mai suna Young Mori.

Mori na daya daga cikin maharban da su ka rika taimakon jami’an tsaro wajen fada da masu garkuwa a cikin dazukan Arewacin Najeriya.

Haka nan shi ma shugaban ayyukan gudanarwar kungiyar mafarautan mai suna Salisu Wobkenso, ya tabbatar da kisan da aka yi wa shugaban su Mori.

Ya tabbatar da cewa a dajin Kaduna aka kashe shi.

“Wannan labari ne mai dauke da bakin ciki a gare mu mafarauta. An kashe Young Mori, daya daga cikin maharban mu na jihar Adamawa. Mori wanda ya fito daga Karamar Hukumar Guyu, ya gamu da ajalin sa yayin arangama da barayin shanu a cikin dajin Kaduna.” Inji shi.

Wobkenso dai bai yi karin haske ba, amma ya ce maharban jihar sa na cike da zaman alhini da jimamin wannan babban rashi da aka yi.

“Gwarzo, Janar Young Mori ubangiji ya yi maka rahama. Ka amsa kira, ta tafi amma b aka rabu da mu ba. Domin za ka ci gaba da kasancewa cikin zukatan mu. Allah ya kyautata kabarin Zwalka Nungurau.” Inji Johnson Gwadamdi.

‘’Duniya babban fagen taka rawa ce. Ka sha fada cewa akwai matasan zaratan Lunguda wadanda su ka fi ka jarumta. To mu dai kam mun shaida ta ka jarumtar. Ka zo duniya ka taka rawar ka, kuma ka bar duniya. Ubangiji ya sanyaya kabarin babban gwarzo,’’ Addu’ar Stephen Gyand.

Share.

game da Author