Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa babban dalilin da ya sa gwamnan jihar Kano wanda ya gaje shi ya kasa zaune ya kasa tsaye a lokacin sarki Sanusi shine, tsananin kiyayya da fargaban an fi shi.
Kwankwaso wanda ya fadi haka a takarda wanda kakakin sa Ali Muhammad ya fitar ranar Laraba, ya ce izzar sarki Sanusi, salon mulkin sa da cika ido yake firgita Ganduje ya sa ba zai iya zama kujerar mulki, Sanusi na mulkin Kano ba
” Kawai ya shirga wa mutane karya ne cewa da yayi wai saboda Jonathan ne ya tsige Sanusi. Babu gaskiya a wannan zance ta sa. Shi dai ya fadi gaskiya, kalan sa ne ba irin kalan Sanusi ba, kuma abin na gigita shi.
” Sannan kuma da irin kushe bashin Dala milyan 1.8 da ya nemi ciwo wa domin wai yin titin jirgi mai amfani da wutan lantarki a tsakiyar Kano, wanda sarki Sanusi ya kushe. Wannan abu yayi matukar bata wa gwamna Ganduje rai, saboda gaskiya da sarki Sanusi ya gaya masa.
A karshe Kwankwaso ya ce bayan haka sai Ganduje ya tsige shi sannan ya kirkiro sabbin masarautu a Kano har kuda hudu, kuma ya nada wadanda zai iya jujjuyawa ba wadanda za su fadi masa gaskiya ba.
Discussion about this post