Rahoton hukumar NCDC da take fitarwa a duk mako ya nuna cewa jihar Kogi ta yi wa mutum 425 ne kacal gwajin Korona tun bayan barkewar cutar a Jihar.
Wannan sakamako ya sha bambam da kurin da gwamnan jihar yayi cewa wai jihar ta tsananta gwajin cutar babu kakkautawa, inda take yin gwajin korona har a kasuwanni, tashoshin motoci, makarantu da wuararen da jama’a ke taruwa.
Shi dai gwamna Yahaya Bello ya ce Korona, tatsuniya ce, abinda ke damun ‘yan Najeriya sun fi Korona.
Gwamnan Bello ya soki yadda gwamnatin Najeriya ta ke biye wa kasashen duniya game da annobar Korona da ake fama da ita a kasar nan da duniya baki daya.
Gwaman Yahaya Bello ya ce bai ga dalilin da zai sa gwamnatin Najeriya ta rika kashe makudan kudade da sunan wai ana yaki da yaduwar korona a kasar nan ba.
” Idan ana sanyi a kasashen Turai da Amurka suna saka kayan sanyi mu kuma a kasar nan muna saka kaya wanda ba na sanyi ba. A najeriya fanka da AC muke sakawa saboda zafi. Menene zai sa dole sai yadda turawa suke so muma a wannan yankin za miu yi.
” Ba mu da cutar Korona a jihar Kogi saboda haka ba za mu kirkiro ta da karfin tsiya ba. Kuma mun yi wa mutane da dama gwaji a jihar mu, babu wanda aka samu ya kamu da cutar a jihar.Bamu da Korona wani ba zai zo ya hakikance ewa sai dole mun ce muna da masu cutar ba.
” Idan aka ce za a rika yi wa mutane Kulle, wato zaman gida dole, za a yi ta samun matsala, mutane za su rika mutuwa saboda wahala. Korona Kasuwanci ne kawai ake yi da ita wanda mu bamu bukatar irin wannan kasuwancin a kasar nan, kawai sai narka kudade kae yi da sunan wai dakile yaduwar Korona.
Gwamna Yahaya ya kara da cewa a yanzu haka ana cewa za a tara naira biliyan 540 don siyo maganin rigakafin cutar. wanda da ayyukan raya kasa aka saka wa da an samu ci gaba a kasar nan.
” Ina gina katafaren asibiti a jihar Kogi, mun kiyasta za mu kashe naira biliyan 4.6. Idan za a kashe wa kowacce jiha a kasar nan naira biliyan 10 akalla, don gina irin wannan asibiti, da mun ciwo karfin wahalhalun rashin lafiya da mutanen mu ke fama dashi maimakon muje mu siyo wa kan mu gaibi.
” Korona ko da magani ana warkewa idan dai ba wata matsala aka samu ba. Haka kuma Bankin Kasa ya bayyana cewa an kashe sama da naira Tiriliyan 3 wajen yaki da korona a kasar nan, wadannan kudade da ayyukan cigaba a ka yi a kasa da yafi.
Discussion about this post