Kungiyar ‘Advocacy for the Advancement of Peace and Harmony in Afrika (ADAPHAI), ta yi kiran a gaggauta kafa dokar-ta-baci a Jihar Barno.
Kungiyar ta hakan ne kawai zai takaita kisan jama’a wadanda ba su ji ba, ba su gani ba da Boko Haram ke yi a Shiyyar Arewa maso Gabas.
ADAPHAI ta kara da cewa ta damu kwarai da irin wasareren da Majalisar Dattawa da ta Tarayya su ke yi dangane da kashe-kashe da kassara mutane da ke ci gaba da yi a jihar jihohin Arewa maso Gabas.
Da ya ke magana a taron manema labarai a Cibiyar ‘Yan Jarida ta Jihar Oyo da ke Igayanku, Ibadan, babban birnin jihar, Shugaban ADAPHAI, Sulaimon Suberu, ya ce tuni ya kamata a ce ‘yan Majalisar Najeriya sun labubo hanyar da za a yi amfani da ita wajen magance ta’addanci a Arewa maso Gabas.
Suberu ya ce kakabin da wasu su ka rika yi na cire Shugabanin Tsaro saboda sun gaza, wannan a cewar sa duk harbin iska ne.
Ya ce yaki da mutane masu hakikanin akida ya Boko Haram abu ne mai bukatar yi masa cikakken nazari a bangaren sojoji.
“An kasa kawar da ta’addanci musamman a jihar Barno, ba don komai ba saboda rabi-rabi sojoji ke yakin, ba su ke da wuka da naman komai ba.
Ya ce kakaba dokar-ta-baci ne mafita domin hakan zai bai wa sojoji damar yin komai gaba-gadi.
Ya ce, “kafa dokar-ta-baci zai ba sojoji damar kutsawa ko’ina su ragargaji ‘yan ta’addata a yi gumurzun a-yi-ta-kare.
“Mu na kuma kira ga Majalsar Kasa su danne zuciyar su, su kawar da siyasa da cin dunduniya, su goyi bayan kafa dokar-ta-baci a jihar Barno, domin sojoji su ji saukin fita gar-da-gar su kakkabe ‘yan ta’adda, kowa ya huta.” Inji Suberu.
Discussion about this post