Kungiyar Miyetti Allah ta taya Kiristoci murnar Kirsimeti, ta yi kiran zaman lumana a tsakanin su

0

Kungiyar Kare Muradin Fulani Makiyaya, Miyetti Allah, ta taya Kiristoci murnar zagayowar bukukuwan Kirsimeti, tare da fatan wanzuwar zaman lumana a tsakanin bangarorin biyu.

Shugaban Miyetti Allah ma Kudu maso Gabas, ya yi kiran Kiristoci su rika yin koyi da tarbiyyar Yesu Almasihu ta hanyar jaddada zaman lumana a tsakanin al’ummar kasar nan.

Shugaban na Kungiyar Makiyaya ta MACBAN na yankin, Gidado Siddiki, ya yi wannan bayanin a Enugu, cikin takardar da ya fitar, inda ya yi tuni da muhimmancin zaman lafiya a kasar nan.

Siddiki ya ce koyi da kuma bin turbar ta Isa Almasihu za ta inganta zaman lafiya da juna a tsakanin mabambantan al’ummomi a kasar nan.

“Shekara ta sake zagayowa, lokacin da Kiristoci ‘yan uwan mu maza da mata ke karakainar tafiya gida a fadin kasar nan, domin bukukuwan Kirsimeti.

“Don haka Kungiyar Miyetti Allah Shiyyar Kudu maso Gabas na yi wa daukacin matafiya garuruwan su domin bukukuwan Kirsimeti fatan sauka lafaiya.

“Yan uwan mu da ke wadansu garuruwa da su ka dawo nan Kudu su ka same mu, mu na yi masu barka da zuwa.

Daga nan Siddiki ya yi kira ga gwamnonin yankin su kare dukiyoyi da rayukan jama’a.

Ya ce shekarar 2020 ta zo, kuma ga ta za ta wuce, amma ta bar baya da kura sosai. Sai ya jinjina wa ‘yan Najeriya saboda juriyar da su ka nuna ga kalubalen da su ka fuskanta cikin 2020.

“Muna godiya ga gwamnatocin wadannan jihohi da suka ba mu wuraren yin sana’ar mu. Kuma muna kara jan hankalin muhimmancin zaman lumana a tsakanin juna.” Inji Siddiki.

A karshe ya yi addu’ar Allah ya bada lafiya da zama lafiya, yalwa da dimbin arziki a cikin 2021 mai zuwa nan da mako daya.

Share.

game da Author