Kukah ya karyata cewa ya nemi a yi juyin mulki

0

Babban Limamin Darikar Kotolika na Sokoto, Bishop Mathew Kukah, ya karyata masu cewa ya nemi a yi juyin mulki.

Kukah ya karyata masu cewa ya nemi a yi wa Gwamnatin Buhari juyin mulki, daidai lokacin da kungiyar kare muradun musulunci ta HURIWA ta nemi a tsige shi daga cikin ‘yan kwamitin zaman lafiya na kasa.

An ruwaito Kukah ya yi wannan karin haske a ranar Talata, a lokacin da ya ke yi wa manema labarai karin haske a ranar Talata.

Sabani ya taso bayan da ya ce “da wani dan Arewa wanda ba Musulmi ne ke mulki ba, kuma ya ke nuna bambanci ko da kadan kyas daga irin yadda Buhari ke yi, ko da kankani ne, to da tuni an kifar da gwamnatin sa, kuma da tuni ana yaki.”

Ra’ayin da Kukah ya furta kan alkiblar gwamnatin Buhari ya janyo cece-ku-ce a kasar nan, inda ra’ayin malamai ya bambanta, haka ra’ayoyin al’ummar Najeriya ya rabu biyu. Daga masu goyon bayan sa cewa ya fadi gaskiya, sai masu sukar sa.

Amma a ranar Talata Kukah ya bayyana wa manema labarai cewa ba shi da matsala da Buhari, amma ya na da matsala da tsarin mulkin da ya ke yi wa Najeriya.

“Wasu jaridu ba su yi min adalci ba, da har su ka buga cewa ya nemi a yi juyin mulki. Ba ni da wani haushi ko nifaka a kan Buhari kankin kan sa.

“Na dai ce ba zai yiwu mu yarda a rika amfani da addini ana siyasa ba a matsayin cin burin siyasa ba.”

Shugaban Kungiyar MURIC, Ishaq Akintola ne ya nemi a cire Kukah daga kwamitin samar da zaman lafiya.

Haka ita ma Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa rashin daraja da rashin kana’ar zici ke sa shugaban addini zai yi amfani da ranar Kirsimeti sukutum ya rika ruruta wutr rikici da kiyayya a cikin kasa.

Wannan gargadinne ga Bishop na Darikar Katolika, Hassan Kuka, wanda gwamnati ta ce maimakon ya yi amfani da ranar Kirsimeti ya yi kiraye-kirayen zaman lafiya, sai ya yi amfani da ranar ya rika zuzuta fitina da raba kan al’ummar Najeriya.

Kukah dai a sakon sa na ranar Kirsimeti, ya bayyana cewa Buhari ba ya komai sai nuna kabilanci, wajen nade-naden sa.

Ya ce “da wani dan Arewa wanda ba Musulmi ne ke mulki ba, kuma ya ke nuna bambanci ko da kadan kyas daga irin yadda Buhari ke yi, ko da kankani ne, to da tuni an kifar da gwamnatin sa, kuma da tuni ana yaki.”

Sai dai kuma a sanarwar da Ministan Yada Labarai Lai Mohammed ya yi, ya bayyana gargadi ga shugabannin addinai su daina furucin hauragiya, wand aka iya haifar da mummunan sakamako.

Kakakin Yada Labarai na Lai Mohammed, Segun Adeyemi, ya fitar da takardar Minista mai dauke da cewa, yayin da shugabannin addinai ke da hakkin fadar gaskiya ga shugabannin da ke kan mulki, to kada ya kasance an lullube wannan gaskiyar a cikin mayafin fushi, kiyayya, raba kan jama’a da kuma kokarin ruruta fitinar rikicin addini.

” Kawo batun juyin mulki a cikin bayanan sa da kuma nuna wani addini a ce ya na tayar da fitina, ba abin alheri ba ne ga shugabannin addinai, musamman a wannan lokaci na hutun Kirsimeti da aka bukatar masu wa’azi su yada kokarin bukatar zaman lafiya da juna.” Inji Lai.

Lai y ace duk mai kiran sauya gwamnati ba ta hanyar zabe ba, ba kiran a yi juyin mullki kadai ya ke yi ba, ya na kira ne har ma a dagula kasa baki daya.

Share.

game da Author