Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi kira ga yaran makarantan sakandaren Kankara da aka ceto daga hannun ‘yan bindiga da su manta abinda ya faru da su su maida hankali wajen karatu.
Buhari ya hori yaran dazamanto masu da’a sannan su fifita karatun su fiyae da duk wani abu da za su yi musamman a yanzu da suke yara kanana.
Wadannan sune kalaman da Buhari yayi a lokacin da ya ke jawabi ga kubutattun daliban makarantan Kankara da aka ceto daga hannun ‘yan bindiga ranar Alhamis.
” Ni dinnan da kuke gani na yi gwamna, nayi minista sannan kuma na yi shugaban kasa gashi har sau biyu. Hakan ya yiwu ne saboda karatu da na dage nayi, wadanda basu yi ba a lokacin shanun su ya kare, sannan babu goni yanzu na noma kamar da.
” Na taho Katsina daga Daura domin in ganku kuma in nuna muku farinciki na kan dawo da ku da aka yi daga hannun ‘yan bindiga. Ku tabbata kun ba mara da kunya, kun jajirce a wajen karatunku sannan ku maida hankali matuka.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda gwamnatin Katsina karkashin Aminu Bello Masari suka ceto yaran makarantan daga hannu yan bindiga da suka arce da su.