Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da belin Olisa Metuh, tsohon Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar PDP a kan naira milyann 250.
Mai Shari’a Nkeonye Maha ya bada belin sa bayan da lauyoyin sa a karkashin jagorancin Oyechi Ikpeazu su ka shigar da neman beli a ranar 21 Ga Disamba.
Sun shigar da neman belin ne bayan gungun masu shari’a na Kotun Daukaka Kara sun bayyana soke daurin shekaru bakwai da Kotun Tarayya a karkashin Mai Shari’a Idang Agbang ta yi wa Metuh, cewa bai yi masa adalci ba, domin kirikiri ya nuna ya na da nifaka a kan wanda ya daure din.
Da ya ke bada belin sa, Maha ya ce a kasance wani mutum ne mai mutunci ba dan jagaliya ne zai karbi belin Metuh ba. Sannan kuma ya kasance mutumin ya na da kadara a Abuja wadda ba ta kasa kaiwa naira milyan 250 ba.
Mai Shari’a ya ce da zaran an cika sharuddan beli, to a gaggauta sakinn sa tarecda sakar masa fasfo din sa na fita waje.
Sannan kotu ta ba shi damar fita waje ya nemi magani ko ganin likita, amma kada ya wuce kwanaki 45.
PREMIUM TIMES HAUSA ta bada labarin kotu ta soke hukuncin daurin shekara bakwai da aka yi wa Olisa Metuh saboda rashin adalci a hukuncin.
Tuni dai har ya yi watanni 10 a gidan kurkuku, daga ranar da aka daure shi, cikin Fabrairu, 2020.
Kotun Daukaka Kara ta soke hukuncin daurin shekaru bakwai da wata kotu ta yi wa tsohon Kakakin Yada Labarai na jam’iyyar PDP, Olisa Metuh, bisa kama alkalin da ya yanke masa hukuncin da nuna bangaranci a shari’ar.
Manyan Alkalai uku a Kotun Daukaka Kara sun hakkake cewa alkalin da ya daure Olisa Metuh daurin shekara bakwai a kotu, bai yi masa adalci ba, saboda ya nuna bangaranci.
An dai daure shi shekara bakwai ne a gidan kurkuku a cikin watan Fabrairu, 2020.
Babban Mai Shari’a Stephen Adah shi ne ya jagoranci sauran alkalai biyu, wadanda su ka soke hukuncin da aka yi wa Metujh, tare da cewa a sake shari’ar daga farko.
Sun bada hukuncin cewa a maida shari’ar ga kowane Alkalin Babbar Kotun Tarayya, amma banda mai shari’a Okon Abang, wanda ya daure shi shekaru bakwai.
Babban Mai Shari’a Adah a Kotun Daukaka Kara, ya ce “irin furucin da Abang ya rika yi a lokacin hukunta Metuh, duniya ta tabbatar da cewa ya na kullace da shi kua ziciyar sa cike ta ke da nifaka a kan Metuh.”
Ya ce bai kamata mai shari’a ya goyi bayan wani bangare ba a wajen yanke hukunci. Abin kuma inji shi, rashin adalci ne karara.
Ya kara da cewa irin wannan cin kashi da rashin mutunci da alkalai ke yi, ba abin da za a ci gaba da zura ido ba ne na faruwa a kasar nan.
Ya ce rashin adalci ne mai shari’a ya tauye wa wanda ake wa shari’a hakkin sa ta hanyar nuna masa bambanci da bangaranci.
Adah ya kara da cewa Mai Shari’a Abang ya zubar da kima da martabar kotu a idon duniya. Saboda haka ba za a kyale hukuncin da ya yi wa Metuh ya zama karbabbe ba.