Korona ta fasa taron Babban Hafsan Sojojin Najeriya na shekara-shekara a Abuja

0

Babban Hafsan Sojojin Najeriya Tukur Buratai ya soke sauran shirye-shiryen da su ka rage na Taron Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya da ya aka shirya.

An tashi daga taron babu shiri, saboda an samu mai cutar korona a cikin mahalarta taron.

Kakakin Sojojin Najeriya Sagir Musa ne ya fitar da wannan sanarwa a ranar Alhamis.

Sagir ya ce an samu mai dauke da cutar a ranar Alhamis.

Sanarwar ta umarci duk wani wanda ya san ya halarci taron da ya gaggauta killace kan sa, kamar yadda dokar da gwamnatin tarayya ta gindaya.

Haka nan kuma Janar Buratai ya sanar cewa an hana duk wani da ya halarci taron halartar zuwa daurin auren dan sa Hamisu Buratai, wanda za a yi a ranar Juma’a.

Buratai ya yi wa kowa fatan alheri, amma ya ce duk wanda ya je taron, to an dauke masa nauyin halartar daurin auren dan sa.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –134, FCT-180, Kebbi-45, Adamawa-26, Filato-16, Enugu-14, Taraba-14, Gombe-12, Nasarawa-8, Yobe-8, Rivers-5, Ogun-5, Kwara-2, Ekiti-2, Sokoto-2 da Osun-1
Yanzu mutum 70,669 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 65,242 sun warke, 1,184 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 4,243 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 24,238, FCT –7,716, Oyo – 3,747, Edo –2,724, Delta –1,827, Rivers 3,075, Kano –1,841, Ogun –2,275, Kaduna –3,502, Katsina -1,069, Ondo –1,728, Borno –758, Gombe –1,047, Bauchi –792, Ebonyi –1,055, Filato – 3,937, Enugu –1,355, Abia – 926, Imo –681, Jigawa –340, Kwara –1,146, Bayelsa –465, Nasarawa – 539, Osun –962, Sokoto – 184, Niger – 298, Akwa Ibom – 362, Benue – 501, Adamawa – 287, Anambra – 290, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 108, Ekiti – 386, Taraba- 195, Kogi – 5, da Cross Rivers – 90.

Share.

game da Author