KORONA: Saura mutum 70 wadanda suka kamu ranar Laraba su cika 1000 cif, mutum 930 suka kamu

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 930 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Laraba.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –279, FCT-179, Filato-62, Kaduna-54, Kano-52, Katsina-52, Imo-42, Jigawa-42, Rivers-38, Kwara-30, Nasarawa-19, Yobe-15, Ogun-13, Borno-10, Oyo-9, Niger-9, Ebonyi-6, Bauchi-6, Edo-5, Taraba-4, Sokoto-2 da Cross River-2.

Yanzu mutum 75062 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 66775 sun warke, 1,200 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 7,087 ke dauke da cutar a Najeriya.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 25,436, FCT –8,908, Oyo – 3,773, Edo –2,747, Delta –1,829, Rivers 3,217, Kano –1,965, Ogun–2,348, Kaduna –4,098, Katsina -1,289, Ondo –1,751, Borno –768, Gombe –1,104, Bauchi –860, Ebonyi –1,075, Filato – 4,099, Enugu –1,363, Abia – 973, Imo –730, Jigawa –340, Kwara –1,275, Bayelsa –471, Nasarawa – 581, Osun –965, Sokoto – 210, Niger – 298, Akwa Ibom – 364, Benue – 501, Adamawa – 329, Anambra – 294, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 123, Ekiti –396, Taraba- 203, Kogi – 5, da Cross Rivers – 92.

Ministan Lafiya, Osagie Ehinare ya bayyana cewa akwai yiwuwar Najeriya ta samu maganin rigakafin Korona a cikin watan Janairu mai zuwa.

Ehinare ya ce dama kuma tuni kasar ta shiga yarjejeniya da Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya, da kamfanin Gavi da zaran maganin ya fito za a wadata Najeriya da shi.

Sai dai kuma bai fadi yawan maganin da za a siyo ba.

” Muna sa ran cewa za mu samu maganin, komai kankanta shi, domin suma kasashen da ke hada maganin na bukatarsa.

Baya ga siyo maganin da za a yi, tsadar sa shima wani abinda za mu duba ne. Sannan kuma wajen ajiya. Maganin na bukatar wajen ajiya mai san karan sanyi wanda mu a kasar nan bamu da irin wadannan na’ura.

Ehinare ya ce shi kansa wurin ajiyan sai an siya.

” Akwai maganin da za mu iya ajiye a firjin mu, da wadanda za mu siyo mu saka su a ciki, sai dai wadanda ke bukatan a ajiye su cikin firji mai dankaran sanyi sai dole an siyo su wadannan firji, Su ma kuma tsadan tsiya suke da shi.

Ya ce gwamnati za ta garzaya wasu kasashen da ke hada maganin domin a siyo su da yawa domin mutanen kasa.

Share.

game da Author