Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 1,145 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Alhamis.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Alhamis sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –459, FCT-145, Kaduna-138, Filato-80, Katsina-70, Gombe-52, Niger-31, Kano-23, Bayelsa-21.
Bauchi-18, Ondo-18, Rivers-17, Ogun-12, Oyo-12, Edo-8, Nasarawa-8, Ebonyi-7, Osun-6, Ekiti-5, Kebbi-5, Borno-4, Jigawa-3, Akwa Ibom-2 da Anambra-1.
Yanzu mutum 76,207 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 67,110 sun warke, 1,201 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 7,896 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 25,895, FCT –9,053, Oyo – 3,785, Edo –2,755, Delta –1,829, Rivers 3,234, Kano –1,988, Ogun–2,360, Kaduna –4,236, Katsina -1,359, Ondo –1,769, Borno –772, Gombe –1,156, Bauchi –878, Ebonyi –1,082, Filato – 4,179, Enugu –1,363, Abia – 973, Imo –730, Jigawa –340, Kwara –1,275, Bayelsa –492, Nasarawa – 589, Osun –971, Sokoto – 210, Niger – 338, Akwa Ibom – 366, Benue – 515, Adamawa – 329, Anambra – 295, Kebbi – 143, Zamfara – 79, Yobe – 123, Ekiti –401, Taraba- 203, Kogi – 5, da Cross Rivers – 92.
Bayan haka Sanata Dino Melaye, gargadi ‘yan Najeriya da gwamnatin Najeriya cewa kada su kuskura su biye wa turawa su amshi maganin rigakafin Korona, su dirka wa mutanen Najeriya.
Dino ya ce wannan magani ba gaskiya ba ne. Ya ce zuwa yanzu da aka dirka wa wasu a kasashen waje duk sun mutu cikin kwana uku.
” Ina kira ga mahukunta a kasar nan da na kasashen Afrika, cewa kada su yarda a shigo mana da wannan magani na Korona, domin ba gaskiya bane. Maganin kashe mutane yake yi. Ana so ne a yi gwajin shi a jikin bakaken fata, mu yi ta mutuwa.
” Muna nan a duniya Kansa, Kanjamau, Ciwon Siga na ta kashe mutane sama da shekaru 40 amma ba a taba samu rigakafin sa ba sai yanzu kwatsam kawai a ce wai an samo maganin lokaci guda. Wannan ba gaskiya bane.
Sai dai kuma Dino bai fadi ko a ina ne ya ga an mutu ba ko kuma da me ya dogara ga.
Ba shi kadai ba akwai wat ‘yar kasar Amurka wanda likita ce da ta koka kan rashin ingancin wannan magani na Korona a jikin mutane. Ta gargadi mutane kada su amshi maganin.
A Najeriya dai ana samun hau-hawan alkaluman wadanda suka kamu da cutar yanzu. Abin ya kai ga har an fara rurrufe makarantu da kuma saka dokoki domin kiyaye wa.