Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 1,016 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Laraba.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –434, FCT-155, Filato-94, Kaduna-56, Rivers-56, Oyo-30
Nasarawa-27, Zamfara-25, Abia-22, Enugu-18, Kano-18, Bayelsa-15, Edo-14, Ogun-11, Borno-10, Ebonyi-10, Jigawa-7, Anambra-4, Delta-3, Niger-3, Osun-3.
Yanzu mutum 86,576 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 73,322 sun warke, 1,278 sun rasu.Sannan kuma zuwa yanzu mutum 11,975 ke dauke da cutar a Najeriya.
A ranar Talata, mutum 794 suka kamu a Najeriya, jihohin Legas, Kaduna, Filato, Sokoto, Kwara da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 29,618, FCT –11,588, Oyo – 3,939, Edo –2,866, Delta –1,882, Rivers 3,459, Kano –2,234, Ogun–2,468, Kaduna –5,127, Katsina -1,618, Ondo –1,807, Borno –806, Gombe –1,272, Bauchi –978, Ebonyi –1,107, Filato – 4,849, Enugu –1,382, Abia – 1,005, Imo –748, Jigawa –403, Kwara –1,414, Bayelsa –534, Nasarawa –765, Osun –1,008, Sokoto –331, Niger – 413, Akwa Ibom – 434, Benue – 532, Adamawa – 391, Anambra – 312, Kebbi – 173, Zamfara –119, Yobe – 187, Ekiti –410, Taraba- 211, Kogi – 5, da Cross Rivers – 169.
Hukumar Babban Birnin Tarayya, Abuja ta bayyana cewa jami’an kula da lafiya 476 ne su ka kamu da cutar korona a Abuja, yayin da cutar ta yi sanadiyyar ajalin likitoci hudu wadanda ba su cikin wannan lissafi.
Sanarwar ta kara da cewa mutuwar baya-bayan nan ta wata mata ce jami’ar kula da lafiya.
Sanarwar ta ce wadanda su ka kamu da cutar sun hada ma’aikatan kiwon lafiya, nas-nas, jami’an kula da dakin gwaji, direbobi da ma’aikata na yau da kullum.
Sanarwar ta ce wannan cuta ta ci rayukan likitoci hudu, daga cikin su kuma wata mata ce ta rasu a baya-bayan nan.
Kakakin Yada Labarai na Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja, Muhammad Bello ne ya fitar da wannan sanarwa, ranar Talata a Abuja.
Ya kara da cewa duk da wannan kaluble da ake fuskanta, dukkan asibitocin Abuja a bude su ke ana ci gaba da ayyukan kula da marasa lafiya tsawon sa’o’i 24.
“Tsawon mako daya kenan rabon da a samu bayanin mutuwar wani majiyyaci sanadiyyar cuutar korona.
“Ya na da kyau jama’a su sani cewa wannan yawan kamuwar jami’ai da cutar korona, ko kadan bai rage aikin gudanarwa da kula da marasa lafiya da ake yi a Abuja ba.’
Idan ba a manta ba, mun buga labarin yadda korona ta kashe likitoci 20 cikin mako daya a fadin kasar nan.