Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 829 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Asabar.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Asabar sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum 296, FCT-291, Kaduna-79, Rivers-40, Kano-35, Nasarawa-25, Bauchi-19, Benue-8, Borno-7, Edo-7, Oyo-7, Sokoto-7, Cross- River-3
Jigawa-3 da Ogun-2
Yanzu mutum 83,576 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 70,495 sun warke, 1247 sun rasu.Sannan kuma zuwa yanzu mutum 11,834 ke dauke da cutar a Najeriya.
A ranar Juma’a, mutum 712 suka kamu a Najeriya, jihohin Legas, Kwara, Katsina, Bauchi, Filato da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 28,488, FCT –11,057, Oyo – 3,885, Edo –2,826, Delta –1,868, Rivers 3,368, Kano –2,169, Ogun–2,451, Kaduna –4,883, Katsina -1,570, Ondo –1,798, Borno –796, Gombe –1,248, Bauchi –964, Ebonyi –1,097, Filato – 4,459, Enugu –1,382, Abia – 983, Imo –748, Jigawa –392, Kwara –1,379, Bayelsa –519, Nasarawa –690, Osun –1004, Sokoto – 297, Niger – 409, Akwa Ibom – 429, Benue – 532, Adamawa – 355, Anambra – 307, Kebbi – 163, Zamfara – 79, Yobe – 187, Ekiti –409, Taraba- 211, Kogi – 5, da Cross Rivers – 169.
Sanadiyyar gano wata nau’in cutar korona da aka yi kwanan nan a wasu kasashe, gwamnatin Najeriya ta fito da wasu sabbin tsautsaran ka’idoji ga masu shigowa kasar nan daga Ingila da Afrika ta Kudu.
Kodinatan Kwamitin Yaki da Cutar Korona na Kasa, Sani Aliyu ne ya bayyana haka a lokacin da kwamitin sa ke wa manema labarai karin haske kan halin da ake ciki kan korona a kasar nan.
“Daga ranar Litinin 28 Ga Disamba, 2020, duk wasu fasinjoji da za su shigo kasar nan daga Birtaniya da da Afrika kai-tsaye ba tare da sun yada zango wata kasa ba, to sai sun cika Rajistar Sharuddan Tafiye-tafiye na Najeriya a intanet tukunna.
“Dole ya kasance sun cika tambayoyin da za a yi masu a shafin intanet din, kuma su yi firintin na takardar shaidar cewa ba su dauke da cutar korona.
“Sannan kuma ya kasance takardar shaidar ta su ba ta wuce kwana biyar da yin gwaji ba.”
Ya ce za a bude wannan rajista a tashoshin jiragen sama domin fasinjojin da za su shigo daga wadannan kasashe, don a tabbatar cewa sun gabatar da kan su an yi masu gwajin cutar korona a rana ta bakwai da isowar su.
Tuni dai sama da kasashe 40 ne su ka hana jiragen sama sauka kasar su daga Birtaniya, sakamakon gano wata cutar korona wadda ta fi wadda ake fama da ita saurin fantsama da kuma saurin kama mutane.
Wasu kasashen da su ka hana saukar fasinjoji daga Birtaniya, sun hada da Indiya, Pakistan, Rasha, Jordan, Hong Kong da kasashen Turai kusan baki daya.
Su kuwa kasashen Saudiyya da Kuwait da Oman sun rufe kasashen su baki daya, ba shiga ba fita.