Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 474 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Laraba.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –134, FCT-180, Kebbi-45, Adamawa-26, Filato-16, Enugu-14, Taraba-14, Gombe-12, Nasarawa-8, Yobe-8, Rivers-5, Ogun-5, Kwara-2, Ekiti-2, Sokoto-2 da Osun-1.
Yanzu mutum 70,669 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 65,242 sun warke, 1,184 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 4,243 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 24,238, FCT –7,716, Oyo – 3,747, Edo –2,724, Delta –1,827, Rivers 3,075, Kano –1,841, Ogun –2,275, Kaduna –3,502, Katsina -1,069, Ondo –1,728, Borno –758, Gombe –1,047, Bauchi –792, Ebonyi –1,055, Filato – 3,937, Enugu –1,355, Abia – 926, Imo –681, Jigawa –340, Kwara –1,146, Bayelsa –465, Nasarawa – 539, Osun –962, Sokoto – 184, Niger – 298, Akwa Ibom – 362, Benue – 501, Adamawa – 287, Anambra – 290, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 108, Ekiti – 386, Taraba- 195, Kogi – 5, da Cross Rivers – 90.
Bayan haka annobar Korona na cigaba da yaduwa a Nahiyar Afirka wanda zuwa yanzu alkaluma suka nuna cewa sama da mutum miliyan biyu sun kamu da cutar.
Mutum sama da miliyan 1.7 sun warke sannan mutum 48,000 sun mutu a dalilin kamuwa da cutar.
Ofishin WHO dake Brazzaville kasar Kongo ya sanar da haka.
Zuwa yanzu kasashen Afirka ta Kudu, Algeria da Kenya ne kasashe a nahiyar da suka fi kamuwa da cutar.
Kasar Afrika ta Kudu mutum 757,144 sun kamu, 20,556 sun mutu.
A Algeria mutum 70,629 sun kamu, 2,206 sun mutu.
Kasar Kenya ta samu mutum 72,686 da suka kamu da mutum 1,313 da Suka mutu
Discussion about this post