Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 418 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Lahadi.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Lahadi sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –113, FCT-86, Abia-47, Kaduna-39,, Rivers-27, Katsina-22, Benue-14, Oyo-13, Kano-12, Enugu-8, Edo-7, Imo-7, Bauchi-6, Ebonyi-6, Ogun-6, Ondo-4 da Nasarawa-1
Yanzu mutum 73,175 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 66,090 sun warke, 1,197 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 5,888 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 24,952, FCT –8,424, Oyo – 3,760, Edo –2,737, Delta –1,829, Rivers 3,151, Kano –1,904, Ogun–2,328, Kaduna –3,867, Katsina -1,197, Ondo –1,751, Borno –758, Gombe –1,069, Bauchi –808, Ebonyi –1,061, Filato – 3,997, Enugu –1,363, Abia – 973, Imo –688, Jigawa –340, Kwara –1,226, Bayelsa –469, Nasarawa – 562, Osun –965, Sokoto – 192, Niger – 298, Akwa Ibom – 364, Benue – 501, Adamawa – 329, Anambra – 290, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 108, Ekiti –395, Taraba- 196, Kogi – 5, da Cross Rivers – 90.
Idan ba a manta ba, a cikin makon jiya ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya bayyana cewa Kashi 10 bisa 100 na wadanda suka kamu da cutar Korona a Najeriya ƴan kasa da shekara 19 ne.
Ehanire ya kuma ce kimiyya ya nuna cewa tsofaffi musamman wadanda ke da shekaru sama da 60 sun fi kamuwa da cutar da wuri.
Ya ce wadannan mutane na daga cikin rukunin mutanen dake dauke da cutar ba tare da sun nuna alamun cutar ba wanda hakan ya sa za su iya yada cutar ba tare da sun sani ba.
Ministan ya yi kira ga masu makarantu da iyaye da su zage damtse wajen kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar domin Kare ‘ya’yan su a lokacin da za a bude makarantu.