KORONA: Mutum 356 suka kamu ranar Litini a Najeriya

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 356 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Litini.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Litini sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –59, FCT-79, Kaduna-56, Katsina-37, Nasarawa-30, Kano-25, Edo-18, Gombe-14, Kebbi-12 Akwa Ibom-7, Rivers-7, Sokoto-7, Abia-3, Ogun-1 da Cross River -1.

Yanzu mutum 78,790 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 68,483 sun warke, 1,227 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 9,080 ke dauke da cutar a Najeriya.

A ranar Lahadi, Mutum 501 suka kamu a Najeriya, jihohin Kaduna, Legas, Filato da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi zaftaran mutane.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 26,767, FCT –9,706, Oyo – 3,788, Edo –2,786, Delta –1,843, Rivers 3,286, Kano –2,057, Ogun–2,383, Kaduna –4,560, Katsina -1,442, Ondo –1,793, Borno –778, Gombe –1,178, Bauchi –897, Ebonyi –1,091, Filato – 4,262, Enugu –1,376, Abia – 983, Imo –734, Jigawa –386, Kwara –1,296, Bayelsa –497, Nasarawa –630, Osun –979, Sokoto – 235, Niger – 381, Akwa Ibom – 402, Benue – 515, Adamawa – 355, Anambra – 299, Kebbi – 155, Zamfara – 79, Yobe – 164, Ekiti –405, Taraba- 203, Kogi – 5, da Cross Rivers – 94.
Gwamnatin Najeriya ta ce a gaggauta sake bude cibiyoyin killace masu cutar korona, ganin yadda cutar ta sake darkakar kasar gadan-gadan ba sauki.

Ministan Harkokin Lafiya Osagie Ehanire ne ya bayyana haka a wurin taron Kwamitin Dakile Cutar Korona a ranar Alhamis, a Abuja.

Ya ce yin hakan ya zama wajibi, ganin yadda korona ta sake darkakar kasashen Turai gadan-gadan, tamkar wutar-daji.

Ya ce a wannan karo kowa na da rawar da zai taka wajen ganin wannan cuta ba ta sake fantsama ta yi wa al’ummar kasar nan mummunan illa ba.

“Mun ga yadda a ‘yan kwanakin nan ake ta samun karuwar masu kamuwa da cutar korona a kullum a kasar nan. Wannan kuwa ya sa mu tunanin sake barkewar cutar a karo na biyu.

“Dalili kenan na bada umarnin a gaggauta sake bude cibiyoyin killace masu cutar korona da cibiyoyin bayar da magunguna wadanda a baya aka rufe, saboda karancin masu dauke da cutar. Kuma a sake gaggauta kai jami’an lafiya a dukkan cibiyoyin.

Share.

game da Author