Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 324 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Juma’a.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Juma’a sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –115, FCT-110, Kaduna-57, Taraba-9, Akwa Ibom-8, Filato-6, Bauchi-4, Ekiti-4, Kano-4, Katsina-4, Rivers-3.
Yanzu mutum 68,627 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 64,467 sun warke, 1,179 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 2,981 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 23,660, FCT –7,101, Oyo – 3,730, Edo –2,705, Delta –1,824, Rivers 3,009, Kano –1,803, Ogun –2,237, Kaduna –3,302, Katsina -1,034, Ondo –1,728, Borno –745, Gombe – 938, Bauchi –782, Ebonyi –1,055, Filato – 3,910, Enugu – 1,332, Abia – 926, Imo –681, Jigawa – 331, Kwara –1,110, Bayelsa – 454, Nasarawa – 507, Osun –947, Sokoto – 166, Niger – 298, Akwa Ibom – 348, Benue – 496, Adamawa – 261, Anambra – 282, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 100, Ekiti – 377, Taraba- 172, Kogi – 5, da Cross Rivers – 90.
Zuwa yanzu alkaluma sun nuna cewa sama da mutum miliyan biyu sun kamu da cutar a Nahiyar Afrika.
Mutum sama da miliyan 1.7 sun warke sannan mutum 48,000 sun mutu a dalilin kamuwa da cutar.
Ofishin WHO dake Brazzaville kasar Kongo ya sanar da haka.
Kasashen Afirka ta Kudu, Algeria da Kenya ne kasashe a nahiyar da suka fi kamuwa da cutar.
Kasar Afrika ta Kudu mutum 757,144 sun kamu, 20,556 sun mutu.
A Algeria mutum 70,629 sun kamu, 2,206 sun mutu.
Kasar Kenya ta samu mutum 72,686 da suka kamu da mutum 1,313 da Suka mutu