Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 281 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Talata.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Talata sun nuna cewa Legas ta samu karin mutum –123, FCT-64, Kaduna-38, Imo-15, Rivers-11, Filato-8, Ogun-5, Bayelsa-4, Kwara-4, Bauchi-3, Edo-3, Kano-2 da Osun-1
Yanzu mutum 67,838 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 63,430 sun warke, 1,176 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 3,232 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 23,410, FCT –6,868, Oyo – 3,728, Edo –2,699, Delta –1,824, Rivers 2,996, Kano –1,795, Ogun –2,228, Kaduna –3,136, Katsina -1,030, Ondo –1,728, Borno –745, Gombe – 938, Bauchi –773, Ebonyi –1,055, Filato -3,877, Enugu – 1,332, Abia – 926, Imo –677, Jigawa – 331, Kwara –1,106, Bayelsa – 454, Nasarawa – 493, Osun –947, Sokoto – 166, Niger – 298, Akwa Ibom – 339, Benue – 496, Adamawa – 261, Anambra – 282, Kebbi – 93, Zamfara – 79, Yobe – 100, Ekiti – 365, Taraba- 163, Kogi – 5, da Cross Rivers – 90.
Domin samun ingantattun bayanai game da korona a Najeriya gwamnati tare da hadin guiwar UNICEF sun samar da wata layin kira na waya da za a rika samun labarin gaskiya game da cutar.
Mutum zai aika da sakon ‘Coronavirus’ zuwa lambar 24453, daga nan za a aiko masa da sakonni game da cutar da matsayin da duniya ke ciki da kasa Najeriya.
Domin shiga wannan dandali a facebook ko Kuma WhatsApp za a iya aikawa da sakon ‘Coronavirus’ zuwa ga +234 908 740 1607. Ko Kuma ta adireshin U-Report kamar haka @ureportnigeria.
Wakilin asusun UNICEF a Najeriya Peter Hawkins ya gargadi mutane da su cigaba da kiyaye sharuddan guje wa kamuwa da cutar korona cewa yin haka ne kadai mutum zai iya samun kariya daga corona.